EFCC za ta gurfanar da Yahaya Bello a kotu Larabar nan

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) za ta gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, a gaban kotu a ranar Laraba domin fuskantar tuhume-tuhume kan almundahanar kuɗaɗe da rashin gaskiya yayin gwamnatinsa.

Rahotanni da Manhaja ta samu sun bayyana cewa an kama Yahaya Bello ne ranar Talata, 26 ga Nuwamba, 2024, yayin da bincike kan zarge-zargen almundahanar kuɗaɗe ke ci gaba. Wani jami’in hukumar ya tabbatarwa Jaridar Sahara Reporters cewa, “Za a tisa ƙeyarsa zuwa kotu yau Laraba domin fara shari’a.” An tabbatar da cewa ana tsare da shi a hedikwatar EFCC da ke Abuja yayin da ake ci gaba da tambayoyi.

Bello, wanda ya shugabanci Jihar Kogi daga 2016 zuwa 2023, yana fuskantar tuhuma kan almubazzaranci da kuɗaɗen gwamnati, karkatar da dukiya, da kuma amfani da ofis wajen cin amanar jama’a.
Hukumar EFCC ta yi zargin cewa Yahaya Bello da wasu mutum uku, ciki har da ɗan uwansa Ali Bello, sun haɗa kai wajen almundahanar kuɗi da suka kai kimanin Naira biliyan 80.

A sabon tuhume-tuhume da aka shigar ranar 25 ga Satumba, an ƙara yawan kuɗaɗen da ake zargi zuwa Naira biliyan 110.4. Tuni wata babbar kotun babban birnin tarayya da ke Maitama, Abuja, ta ƙi amincewa da roƙon beli da wasu waɗanda ake ƙara tare da Yahaya Bello suka gabatar. Mai shari’a Maryanne Anenih ta bayyana cewa sai an gama wa’adin umarnin kotu kafin a sake duba batun belin.

Bayan haka, EFCC ta sanar da kotu cewa sun amince da sake dawo wa ranar 27 ga Nuwamba, domin ci gaba da shari’a, wato 20 ga Nuwamba wanda wannan lamari bai yi wa lauyan masu gabatar da ƙara daɗi ba. Wannan ne zai bayar da damar gudanar da shari’ar cikin tsari bisa doka.