Daga USMAN KAROFI
Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai bar Abuja a ranar Laraba don kai ziyara zuwa ƙasar Faransa bayan gayyatar da Shugaban Ƙasar Faransa, Emmanuel Macron ya yi masa. Ziyarar ta kwanaki uku tana da nufin ƙarfafa dangantakar siyasa, tattalin arziki da al’adu tsakanin ƙasashen biyu.
Har ila yau, za a mai da hankali kan samar da damarmaki a fannoni kamar noma, tsaro, ilimi, lafiya, matasa da aikin yi, ƙirkire-ƙirkire da sauyin yanayi.
A ranar Alhamis, Shugaba Tinubu da mai ɗakinsa, Sanata Oluremi Tinubu, za su karɓi tarba a gidajen tarihi na sojoji na Les Invalides da kuma fadar Palais de l’Élysée.
Shugaba Macron da mai ɗakinsa, Brigitte, za su jagoranci bikin buɗe taron kafin gudanar da tattaunawar da ta shafi hulɗar ƙasashen biyu.
Wannan ziyarar za ta yi nazari kan dabarun bunƙasa shirin musayar basira don ƙara horar da matasa wajen ƙere-kere, kasuwanci da shugabanci.
Shugabannin biyu za su shiga taruka da ke karkata kan harkokin siyasa da diflomasiyya tare da mayar da hankali kan kuɗi, albarkatun ƙasa, kasuwanci da zuba jari. Haka nan, za su halarci taron Kwamitin Kasuwanci na Faransa da Nijeriya, wanda ke kula da rawar da ɓangaren masu zaman kansu ke takawa wajen ci gaban tattalin arziki. Brigitte Macron da uwargidan shugaban Najeriya za su tattauna batutuwa kan shirin Renewed Hope Initiative da ke tallafawa mata, yara da marasa ƙarfi a Nijeriya.
Daga ƙarshe, Shugaban Tinubu da mai ɗakinsa za su halarci liyafar cin abincin dare tare da Shugaba Macron kafin dawowar su. An kuma bayyana cewa wasu manyan jami’an gwamnati za su raka shugaban Najeriya a wannan tafiya, kamar yadda mai bai wa shugaban shawara , Bayo Onanuga ya sanar a wata takarda a Abuja ranar Talata.