El-Rufai ya musanta ficewa daga APC

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ƙaryata jita-jitar da ake yi cewa ya koma jam’iyyar adawa ta PDP ko wata jam’iyya, yana mai bayyana labarin a matsayin “ƙarya”.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na ɗ, El-Rufai ya ce ya miƙa batun ga lauyoyinsa don ɗaukar matakin doka.

Wani hadiminsa ya bayyana wa manema labarai cewa jita-jitar ba gaskiya ba ce, yana mai cewa aikin masu neman rura wutar rikici ne kawai. 

Rahoton ya ƙara cewa, tsohon gwamnan bai karɓi katin zama memba na PDP daga Unguwar Sarki a Kaduna ba, kamar yadda wasu kafafen yaɗa labarai suka ruwaito.

“Don Allah a yi watsi da ƙaryar da jita-jita game da alaƙata ta siyasa. Na mika wa shugabannin dillalan labaran karya don ci gaba da daukar matakin da lauyoyina za su dauka,” inji tsohon Gwamnan Kaduna.

Wani mai taimaka wa tsohon gwamnan da bai so a buga maganarsa ba, a wata tattaunawa ta wayar tarho tun farko, ya bayyana raɗe-raɗin cewa El-Rufai ya sauya sheƙa zuwa kowace jam’iyyar siyasa a matsayin ƙarya da tsantsar hannun ‘yan ɓarna.

Mataimakin ya ce, “Aiki ne na masu yin ɓarna. Ba na so in yi magana game da sakon da aka buga a dandalin sada zumunta na mai ɓarna, amma rahoton ƙarya ne. Tsohon gwamnan bai koma PDP ko wata jam’iyya ba.”

Wasu kafafen yaza labarai na yanar gizo da masu amfani da shafukan sada zumunta sun ruwaito a ranar Lahadin da ta gabata cewa El-Rufai ya koma jam’iyyar PDP ne domin ya tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027.

Rahoton ya ƙara da cewa tsohon gwamnan ya karɓi katin zama dan jam’iyyar PDP daga Ungwan Sarki da ke ƙaramar hukumar Kaduna ta Arewa.

Idan za a iya yunawa, El-Rufa’i na ta yaɗa jita-jitar sauya sheƙa tun bayan kasa shigar da shi cikin majalisar ministocin Tinubu bayan tantancewar da majalisar dattawa ta yi masa kan dalilan tsaro.

A watan Maris 2024, El-Rufai ya ziyarci sakatariyar jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) da ke Abuja inda ya gana da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Shehu Musa Gabam. Kwanaki ya sake yin wani taro a gidan Abuja na Sanata Abubakar Gada, jigo a jam’iyyar SDP da wasu shugabannin jam’iyyar.

Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Sanata Teslim Folarin ɗan takarar gwamnan jihar Oyo a karkashin jam’iyyar APC a zaɓen 2023 da kuma Sanata Nazif Suleiman jigo a jam’iyyar PDP daga jihar Bauchi da kuma Alhaji Aminu DanAgundi, ɗan siyasa mai nauyi kuma sarki a jihar Kano.

A watan Afrilu, ya fito fili ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu tana kashe kuɗaɗen tallafin man fetur fiye da gwamnatocin baya.

Haka kuma a watan Yuni, El-Rufai ya karɓi baƙuncin Rabiu Musa Kwankwaso, ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, a gidansa da ke Abuja.

Wannan ganawar ta biyo bayan ziyarar da ya kai wa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a garin Daura na jihar Katsina.

Masu sharhi kan al’amuran siyasa na ganin matakin El-Rufai na iya zama wani babban dabarar da wasu ‘yan siyasar arewa ke yi na ƙalubalantar shugaba Tinubu a zaɓe mai zuwa.