El-Zakzaky: Aikin gama ya gama, cewar lauya

*Sarƙaƙiyar da ke cikin shari’ar
*Za mu ɗaukaka ƙara, inji Gwamnatin Kaduna
*Mu diyya za mu nema, cewar ’yan Shi’a
*Bulandar da ta sa kotu sakin malamin

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

An bayyana cewa, hukuncin da Babbar Kotun Jihar Kaduna ta yanke game da shari’ar da aka gudanar kan jagoran ƙungiyar ’yan uwa Musulmi ta IMN, wacce a ke kira da ’yan Shi’a, wato Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, ba za a iya sake ta ba. Don haka aikin gama ya gama.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin wani }wararren lauya mazaunin Kano, Barista Nazir Adam, wanda ya ce, bisa la’akari da sashe na 36 (9) na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya, ya yi tanadin cewa, ba za a iya yi wa mutum shari’a sau biyu kan laifi iri ɗaya ba. Amma sai dai lauyan ya ƙara da cewa, Gwamnatin Jihar Kaduna ta na da damar ɗaukaka ƙara, idan har hukuncin bai yi ma ta ba.

Tun bayan yanke hukuncin dai a ranar Larabar da ta gabata, 28 ga Yuli, 2021, a ke samun kace-nacen ra’ayoyi mabambanta, domin akwai ƙwararrun da ke cewa, tun farko gwamnatin jihar ce ta yi bulanda wajen yanke hukuncin, saboda kotun ta dogara da hujjar da ita kanta gwamnatin ta kafa ne a yayin sallamar sa tare da maiɗakinsa, Malama Zinat, kamar yadda lauyoyinsu su ka buƙata.

Gwamnatin Kaduna ta gurfanar da shi a gaban kotu ne a shekara ta 2018 ƙarƙashin dokar da ta kafa a shekara ta 2017, duk da cewa, laifin da a ke tuhumar sa da shi ya aikata shi ne a shekara ta 2015, wato kafin kafa dokar.

Don haka, lauyoyin shehin malamin sun nemi kotu da ta yi watsi da ƙarar ne bisa dogaro da cewa, laifin ya rigayi dokar. Wannan ya sanya al}alin kotun, Mai Shari’a Gideon Kurada, ya amince da cewa, a lokacin ba laifi ba ne abin da a ke zargin sa da shi, domin dokar ba ta wanzu ba, ballantana a ce ya karya ta.

Da ya ke ƙarin bayani kan yiwuwar ko a yanzu Gwamnatin Kaduna ta na da damar da za ta iya ɗauko dokokin baya, waɗanda su ka rigayi laifin da a ke zargin malamin da shi, don sake gurfanar da shi, Barista Nazir Adam ya ce, hakan ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya, amma su na da damar ɗaukaka ƙara, kamar yadda faru da wata shari’a da a ka taɓa yi tsakanin Gwamnatin Jihar Kano da Nafiu Isyaka Rabiu, inda duk da cewa, Babbar Kotun Jihar Kano ta wanke shi, amma sai Kotun Ɗaukaka Ƙara ta canja hukuncin ta hanyar ɗaure shi wasu adadin shekaru, kuma Kotun Ƙoli ma ta tabbatar da hakan.

Bugu da ƙari, a cikin irin sarƙaƙiyar da ta biyo bayan shari’ar shi ne, rashin biyan diyya ga malamin sakamakon shafe shekaru da dama da ya yi a tsare da kuma rauni da ya samu a lokacin da jami’an tsaro su ka kama shi.

To, amma Barista Adam ya ce, a irin wannan shari’ar ba kasafai kotu ke bayar da diyya, amma malamin da matar tasa su na da damar garzaya wa wata kotun, don neman diyya.

Wannan bayanin ya zo a kan gaɓa, domin kuwa lauyan da ya wakilci Babban Lauya Femi Falana a wajen shari’ar da su ka kare Sheikh El-Zakzaky, wato Barista Marshal Abubakar, ya shaida wa manema labarai a Kaduna jim kaɗan bayan yanke hukuncin cewa, za su nemi a biya malamin diyya.

Idan dai za a iya tunawa, a shekara ta 2015 ne a ka yi artabu tsakanin mabiya tafarkin Shi’a da Rundunar Sojojin Ƙasan Nijeriya a Zariya da ke Jihar Kaduna sakamakon rufe hanya da mambobin Shi’ar su ka yi, su ka kawo cikas ga wucewar al’umma, ciki kuwa har da Babban Hafsan Hafsoshin Ƙasa na Nijeriya, lamarin da ya kai ga rushe zawiyyar malamin, kama shi tare da matarsa, baya ga kashe ’ya’yansa da wasu mabiyansa.

Shekaru biyu bayan kama shi ne, Gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa dokar tayar da ƙayar baya da czuguna wa jama’a a jihar, wacce kuma bayan shekara ɗaya, wato a 2018, ta gurfanar da malamin a ƙarƙashin dokar. Shekaru uku bayan fara shari’ar ne kuma kotun ta wanke shi.

To, sai dai duk da haka, Gwamnatin Jihar ta Kaduna ta yi iƙirarin cewa, ta na shirin ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ɗaukaka Ƙara, kamar yadda lauyan da ke jagorantar shari’ar, Barista Dari Bayero, ya shaidar.

“Kotun ta ce, dukkan shaidun da mu ka gabatar ba su gamsar da ita shaidar da ta nuna cewa mutane biyun sun aikata laifi ba,” inji shi a yayin da ya ke magana da manema labarai, yana mai ƙari da cewa, “wannan ba ya nufin ba za mu iya sake gabatar da shi a gaban kotu ba… tabbas za mu sake yin tuhuma kan mutanen biyu.”

A Nijeriya dai mabiya tafarkin Shi’a na daga cikin tsirarun da su ke zargin Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da Gwamnatin Jihar Kaduna da yi mu su mulkin kama-karya ta hanyar zaluntar su, kodayake sauran al’umma na zargin su da takura rayuwarsu ta hanyar tsare hanyoyi da su ke yi da sunan addini.