Za a yi wa yara milyan 3 rigakafin shan-inna a Kano

Daga HAMISU IBRAHIM

Yara ‘yan ƙasa da shekara 5 su sama da miliyan uku ake sa ran za a yi wa rigakafin cutar shan inna (polio) da sauran cututtuka masu kassara yara ƙanana a jihar Kano daga ran 31 ga Yuli zuwa 3 ga Agustan 2021.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Kwamishinan Lafiya na Jihar, Dr Aminu Tsanyawa, sa’ilin da yake jawabi a wajen taron bita tare da ‘yan jarida a Kano game da shirin yaƙi da cutar.

Dr. Aminu wanda Babbar Sakatariya Amina Aliyu Musa ta wakilta a wajen taron, ya ce za a gudanar da yaƙi da cutar ne a wuraren da aka keɓe don gudanar da shirin sannan jami’ai za su riƙa bi gida-gida don ɗiga wa yara maganin Polio a baki a ɗaukacin ƙananan hukumomi 44 da kihar ke da su.

A cewarsa, an aiwatar da matakan daƙile cutar da dama wanda hakan ya sa akwai buƙatar wayar da kan jama’ar jihar kan tabbatar da yaran da suka cancanta sun samu maganin duk da annobar korona da ake fama da ita.

Ya ce, “Akwai buƙatar saka himma matuƙa yayin shirin don tabbatar da ba a rasa yaro ko guda ba wajen karɓar maganin. Wajibi ne mu sani cewa tsallake wasu yara ba tare da yi musu rigakafin fi yana haifar da sakamako mara kyau wanda hakan zai yi tasiri wajen yaƙi da cutar.”

Jami’in ya ce a ranar 25 ga Agustan 2020 aka ce Nijeriya da nahiyar Afirka sun kuɓuta daga cutar Polio bayan da aka shafe shekar 3 ba tare da an samu wani ɗauke da cutar ba, haka ma a Kano tun a Yulin 2014 aka rabub da cutar a jihar.

Dr. Aminu ya dangata galabar da Kano ta samu a kan Polio da irin ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi wajen cim ma baƙatun jihar da ta sanya a gaba.

A ƙarshe, ya yaba wa tawagar masu gudanar da shirin rigakafi na jihar da sarakuna da shugabannin addini da sauransu waɗanda a cewarsa baki ɗaya sun taka muhimmiyar rawa wajen samun nasara a shirye-shiryen rigakafin jihar.