Ganduje ya amince da kashe Naira miliyan 160 don gina ofishin ‘yan sanda a Getso

Daga WAKILINMU

A matsayin wani mataki na matse ƙaimi game da yaƙi da ‘yan ta’adda da harkokinsu, masu garkuwa da mutane da sauran muggan laifuka a jihar Kano, Gwamnan Jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya ba da kwangila ta Naira milyan 160 domin gina ofishin ‘yan sanda irin na zamani a yankin Ƙaramar Hukumar Gaya da ke jihar.

Ofishin wanda bayan kammalawa za a zuba masa ingantattun kayan aiki na zamani, an ɗauki matakin gina shi ne don daƙile matsalolin ‘yan ta’adda a jihar da kuma kwararar masu aikata manyan laifuka daga wasu jihohi zuwa Kano.

Idan dai za a iya tunawa, a lokautan baya shugaban Ƙaramar Hukumar Gwarzo ya yi ƙorafi tare da nuna damuwarsa kan yadda ake samun kwararar masu haƙar ma’adinai ba a bisa ƙa’ida ba daga Zamfara zuwa ƙauyukan kan iyakar Gwarzo.

Ofishin wanda za a gina shi a garin Getso a yanki Ƙaramar Hukumar Gaya, zai taimaka wajen sha’anin yaƙi da matsalolin tsaron da ake fama da su a yankin Gwarzo da kewaye.

Kwamishinan Muhalli na Jihar Kano, Dr. Kabiru Ibrahim Getso, shi ne ya bayyana haka a wajen bikin ƙaddamar da aikin gina ofishin. Tare da cewa, ginin zai ƙunshi har da rukunin gidaje don amfanin manya da ƙananan jami’an ‘yan sanda, haɗa da masallaci da kuma hasumiyar ba da tsaro.

Ya ƙara da cewa, Gwamna Ganduje ya amince da a samar da wasu abubuwan more rayuwa a yankin da suka haɗa da asibiti da faɗaɗa kasuwar dabbobi ta Getso tare da samar da kwata irin ta zamani don samar da aikin yi ga matasan yankin.

Dr. Getso ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga al’ummar yankin da su bai wa ɗan kwangilar haɗin kan da ya kamata, tare da cewa gwamnati za ta duba ta biya diyya ga dukkan waɗanda lamarin ya shafa, musamman ma tashar motar da aka tashe ta daga yankin.

A nasa ɓangaren, Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano wanda Engr. Bello Sule ya wskilce shi a wajen taron, ya jaddada ƙudurin gwamnatin jihar na samar da abubuwan more rayuwa a sassan jihar baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *