Dalilin da ya sa Gwamnantin Kaduna ta sake maka El-Zakzaky a kotu

Daga AISHA ASAS

Gwamnatin jihar Kaduna ta sake shigar da sabbin tuhume-tuhume na ta’addanci da laifin ja da dokokin hukuma kan jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Ibrahim El-Zakzaky.

Idan ba a manta ba, a Larabar da ta gabata Babbar Kotun Kaduna ƙarƙashin Jastis Gideon Kurada ta wanke El-zakzaky da matarsa Zinat daga tuhume-tuhume guda takwas saboda rashin cancanta.

Sai dai da alama hukuncin da kotun ta yanke bai gamsar da gwamnatin Kaduna ba wanda hakan ya sa tuni ta sake shirya wasu sabbin tuhume-tuhume guda bakwai a kan El-Zakzaky a Babbar Kotun Tarayya a Alhamis da ta gabata.

Daraktan Gabatar da Ƙara na Jihar, Daris Bayero, ya faɗa wa manema labarai cewa sabbin tuhume-tuhumen da ake yi wa El-Zakzaky sun shafi ta’addanci da ne da ja da dokokin hukuma a jihar da ma Gwamnatin Tarayya.

Ya ƙara da cewa, wasu aikata ba daidai ba da ake tuhumar El-Zakzaky da aikatawa sun faru ne tun kafin 2015.

Ya ce da wannan sabbin tuhume-tuhumen da aka yi, kotu za ta ba da umarnin a kamo El-Zakzaky domin jin ta bakinsa.