‘Yan bindiga sun farmaki asibitin Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

‘Yan bindigar da suka addabi sassan jihar Zamfara sun kai hari a Babbar Asibitin da ke Ɗansadau a yankin Ƙaramar Hukumar Maru da ke jihar a Juma’ar da ta gabata.

Shugaban Ƙungiyar Likitoci ta Ƙasa reshen Jihar Zamfara, Dr. Mannir Bature, shi ne ya tabbatar wa manema labarai da harin a wata sanarwa da ya fitar ran Asabar a Gusau.

Dr. Bature ya ce maharan sun shigo ne da nufin kwashe likitoci da malaman jinya da ke aiki a asibitin, sakamakon bincike da aka gudanar hakan ya hana haƙarsu cim ma ruwa, sai dai sun tafi da wani mai kula da ɗakin majinyata da ɗan’uwan wani mara lafiya guda ɗaya.

Ya ƙara da cewa, wasu ma’aikatan asibitin mata su biyu sun ji rauni yayin harin.

Sakamakon faruwar lamarin, Bature ya ce ƙungiyarsu za ta yi taron gaggawa domin tattaunawa kan batun.

Sai dai ya zuwa haɗa wannan rahoto, labarin aukuwar lamarin bai isa gaban ‘yan sandan yankin ba.