Emefiele ya roƙi gafarar ‘yan Nijeriya kan matsalar hada-hadar kuɗi ta intanet

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele ya nemi gafara kan ‘yan Nijeriya kan qalubalen da aka fuskanta kan tsarin hada-hadar kuɗi ta intanet.

Emefiele ya nemi gafarar ne a taron kwamitin tsarin kuɗi na MPC da aka gudanar a ranar Talata a Abuja, inda gwamnan ya aminta da cewa, an samu ƙalubalen wanda a yanzu an warware ƙalubalen.

Da yake amsa tambayoyi akan abin da ya shafi bankuna ganin yadda wasu bankuna a ƙasar Amurka ke durƙushewa, gwamnan ya ce bankuna a ƙasar nan ba za su durƙushe ba kamar yadda aka samu a ƙasar Amurka ba.

Emefiele ya bayar da tabbacin cewa, ɗaukacin bankuna a ƙasar nan, za su ci gaba da samun kariyar da ta kamata.

A cewar Emefiele, babu wani mai ajiya a bankunan da ke ƙasar nan da zai yi asarar kuɗin da ya ajiye tun daga shekarar 2000, inda ya ce, an samu wannan nasarar ne, saboda kyakyawan tsarin da bankin Nijeriya ya samar, mussaman don kare kuɗaɗen masu ajiya a bankunan.

Emefiele ya kuma gargaɗi masu ruwa da tsaki a fannin tafiyar da bankuna a ƙasar nan, da su kwana da sanin cewa, lasisin kafa bankuna da ake ba su dama ce bai wai dole ba ne wanda kuma za a iya karɓewa idan aka aikata ba daidai ba.

A ƙarshen taron na MPC, mahalarta taron sun amince da a ƙara kuɗin haraji zuwa kashi 18 daga wanda ake yi a baya na kashi 17 wanda aka amince a watan Janairu.