Me ya rage wa Matawalle da Ganduje a jihohinsu?

Gwamnan jihar Zamfara, Muhammadu Bello Matawalle na jam’iyyar APC ya sha kaye a hannun ɗan takarar jam’iyyar PDP, Dauda Lawal Dare.

Dauda Lawal ya samu ƙuri’u mafi rinjaye ne a zaɓen kamar yadda hukumar zaven ƙasar ta sanar.

Jihar Zamfara mai fama da rikicin ’yan bindiga, a yanzu ta koma hannun jam’iyyar PDP, wanda mu ke da tabbacin da yardar Allah za ta kawo kan lamarin.

Dama a shekara ta 2019, kotu ce ta bai wa Matawalle kujerar gwamna bayan da ta yanke hukuncin cewa jam’iyyar APC ba ta bi ƙa’ida ba wajen gudanar da zaɓen fitar da gwani.

Gwamnan jihar Zamfara zai bar kujerarsa a fadar gwamnati da ke Gusau a cikin watan Mayu kuma babu tabbas yadda makomar siyasarsa za ta kasance bayan sauka daga mulki ganin cewa bai samu wa’adin mulki na biyu ba.

A ɗaya ɓangaren kuma, tun bayan zaɓen shugaban ƙasa a jihar Kano inda jam’iyyar APC mai mulki ta sha kaye a hannun jam’iyyar adawa ta NNPP, alamu suka nuna cewa gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje sai ya dage idan har yana son ɗan takarar APC, Nasiru Gawuna ya ci zaɓe.

Amma bayan kammala zaɓen gwamna a ƙarshen mako, sai jam’iyyar NNPP ta ƙwace ragamar jihar inda hukumar zave ta ƙasa INEC ta ayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar.

Wannan sakamakon ya nuna cewa Ganduje bai kawo jiharsa ba ga jam’iyyar APC a zaɓen gwamna da kuma na shugaban ƙasa.

A yanzu ta tabbata cewa a cikin watan Mayu jam’iyyar NNPP ita ce za ta shiga fadar gwamnatin jihar Kano a yayin da APC za ta koma adawa.

Ina taya Dauda Lawal Dare a Zamfara, da Abba Kabur Yusuf a Kano murnar lashe zaɓe. Allah Ya taya ku riƙo.

Daga MUNTAZAR MUSA, 08141306201.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *