Wani soja ya yi kuskuren bindige mata da miji da jaririnsu a Neja

Daga AMINA YUSUF ALI

Wani soja a Jihar Neja ya bindige mutane uku ‘yan Jamhuriyar Benin har lahira a yankin Babana da ke ƙaramar hukumar Borgu a jihar Neja.

Ciyaman ɗin ƙararmar hukumar Borgu, Alhaji Suleiman Yarima, wanda ya tabbatar da faruwar al’amarin ya roƙi al’ummar Babana da su kasance cikin lumana a game da kisan da aka yi wa danginsu, tare da ba su tabbacin cewa rundunar sojojin Nijeriya suna kula da lamarin.

Kuma ya ba wa mutanen tabbacin cewa shari’a za ta nuna ikonta.

Wani shaidar gani da ido kuma mazaunin yankin da abin ya faru, Audu Alkali, ya bayyana cewa, an kashe mutanen uku ne a hanyarsu ta dawowa daga kasuwa.

“Sojan ya kashe mutane uku, miji da matarsa da kuma jariri waɗanda suka je kasuwar garin Babana daga Niganji ta ƙasar Benin don cin kasuwa. Baqin al’amarin ya faru ne a hanyarsu ta dawowa daga kasuwar”. Inji Audu Alkali.

Ya ƙara da cewa, musu ne ya sarƙe tsakanin mutumin da sojan, sai sojan ya yi masa barazana da bindiga cikin kuskure kuma ya bindige su dukka ukun har lahira.

Ciyaman Yarima ya bayyana cewa, a yanzu haka an tura wakilai zuwa ga mutanen Niganji na ƙasar Benin don ba da haƙuri ga iyalan waɗanda sojan ya kashe, ya ƙara da cewa, a halin yanzu ana cigaba da bincike a game da musabbabin abinda ya jawo kisan.

“Ina roƙon mutane a kan su nutsu kuma kada su ɗauki doka a hannayensu sannan su ƙyale hukumar da ta kamata ta kula da al’amarin”. Inji shi.

A lokacin da aka tuntuɓe shi a game da batun, Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Neja, DSP Abiodun Wasiu, ya ce shi ba ya ce shi ba shi da hurumin cewa komai a harkar da ta shafi sojoji.