Dole a rage kuɗaɗen da ake ba shugabannin Nijeriya

Ya zama dole a rarrage kuɗaɗen albashi da na alawus-alawus na duk waɗansu zaɓaɓɓun ’yan siyasa tun daga ƙasa har sama. A nan ina nufin tun daga kansiloli har zuwa shugabannin ƙananan hukumomi, sannan da ’yan majalisar jihohi da majalisun gaba ɗayansu.

Daga nan kuma sai a rarrage kuɗaɗen ’yan Majalisar Wakilai da ta Dattawa. Gaskiya kullum ana cewa talakawan ƙasa suna cikin matsin rayuwa amma an ƙasa ganin yaya al’amarin yake, kuma an yi mirsisi an ki fahimtar ababen da gangan da ganganci.

Gaskiyar lamari gwamnati mai ci yanzu tunda ta kama ragamar mulki a shekarar 2015, sai kawai aka wayi gari ta ƙara kuɗaɗen albarkatun man fetur daga Naira 97 zuwa Naira 145 wanda karin ya shallake hankali kuma kananzir da gas duka aka yi musu karin da ya fi na arzikin Kundila.

To, ga masana sun ce an yi haka ne domin tafiyar da gwamnati mafi tsada, wato, ta launin yadda Amurka take yi ‘American System’ to shi ne dalilin ƙarin kuɗin man fetur da dangoginsa. Gaskiya, wannan aqida ta gwamnati ita ta jawo tashin komai cikin Nijeriya, ta janyo komai ya zama jangwam, kuma talakawa suka shiga cikin wahalolin rayuwa.

Abu ne mawuyaci Gwamnatin Muhammadu Buhari ta juyo da baya domin gyara wannan kuskure tunda ’yan siyasar wannan zamani sun rungume ta ce domin lagwadar da ake samu ba wai domin kyautata wa jama’a ba.

Saboda haka, ya zama wajibi kowane ɗan majalisa ya saki rabin kuɗinsa domin taimaka wa ƙasa, haka Shugaban Ƙasa da ’yan majalisarsa da kuma dukkan ministoci. Haka ma gwamnoni da dukkan kwamishinoni da dukkan wanda aka naɗa a siyasance.

Gaskiyar lamari, dole Shugaban Ƙasa ya yi iyakar iyawarsa domin ganin duk ’yan Majalisar Wakilai da na Majalisar Dattawa duk wanda ya karɓi aikin mazabu ‘Constituency Project’ bai yi ba, lallai ya dawo wa gwamnati kuɗaɗenta.

Domin kuwa bai yi aikin ba, saboda haka ya zama dole ya amayar da kuɗaɗen da aka ba shi. Kuma daga ƙarshe rokona ga Gwamnatin Tarayya shi ne a lura da iyakokin ƙasar nan, ba wai kawai a matsa kan shigo da motoci ba ko shinkafa, a’a shigowar baki ratata ba ya zame wa kasa abin alheri domin kashe-kashen bayin Allah sun yi yawa. Saboda haka, dole a hana shigowar bakin haure ta dukkan iyakokinmu duk da an ce daga na gida ake cin yakin gida.

Muhammadu Buhari a matsayinka na Shugaban Ƙasa da gwamnonin jihohi ku tashi tsaye domin ceto ƙasar nan kada ta wargaje, saboda son kai na waɗansu mutane ƙalilan waɗanda idan ba su samu mulki ba, sai dai Nijeriya ta shiga halin ni-’yasu. Allah Ya tsare, Ilahee Ameen.

Amma dai rage kuɗaɗen albashi da alawus-alawus na waɗanda muka ambata zai zama alheri ga ƙasarmu Nijeriya, sannan a rage kuɗaɗen man fetur da dangoginsa. Haka zai bada damar warware matsalolin Nijeriya da jama’arta.

Wassalam; saƙo daga Ahmad Musa, 07041094323.