Zaɓe sai haƙuri fa!

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Wasu na kuka wasu na dariya don rashin gamsuwa ko gamsuwa da sakamakon babban zaɓen Nijeriya kama daga na Shugaban Ƙasa zuwa na gwamnoni, ’yan majalisar tarayya da na jiha da a ka kammala in ka deve wajajen ƙalilan da hukumar zaɓen ta ayyana cewa zaɓe bai kammala ba.

Duk abun da za a ce a zaɓe sai an samu wanda ya lashe da kuma wanda bai lashe ba. Wani abu dai shi ne kowa zai so a ce shi ya lashe. Shin zaven an yi adalci ko ba a yi adalci ba, wannan ba shi ne karo na farko da a ke gudanar da zave a Nijeriya ba. Hatta su kan su shugabannin hukumar zaɓen na aiki ne na tsawon wasu shekaru kafin su koma gefe.

Wasu daga cikin su na samun suka a mafi akasari wasu kuma ƙalilan na don samun yabo. Hakanan wasu sai tashin zance za ka ji a na magana a kan su. In za a tuna kamar Farfesa Maurice Iwu ba a tashi tuno shi a bayan-bayan nan sai lokacin da tsohon shugaba Obasanjo ya buƙaci a soke sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Wasu masu shrahi su ka tuno yafda Iwu ya sanar da sakamakon gabanin kammala tattara ƙuri’a ma. Abun tarihi a wancan zaɓe wanda a ka aiyana a matsayin wanda ya yi nasara wato marigayi Umaru Musa ’Yar’adua ya zayyana zaɓen na sa da cewa an samu matsaloli ko ba a gudanar da shi bisa cika dukkan ƙa’idoji ba.

An je har Kotun Ƙoli inda nan ma a ka samu alƙalai 3 su kja soke zaɓen 3 su ka marawa zaɓen baya don haka marigayi babban alqali a lokacin Idris Legbo Kutigi ya marawa zaɓen baya. Shugaba ‘Yar’adua ya kafa kwamitin gyara lamuran zaɓe ƙarƙashin tsohon babban alƙali Muhammad Lawal Uwais da zuwa yau duk wani gyara mai ma’ana da ya faru a zaɓen ya biyo bayan wancan aikin ne.

Kamar kuma yadda na baiyana a rubutun da na yi a baya cewa in ban ce duka ba, akasarin ’yan siyasa na da ɗabi’a iri ɗaya da ya ke zama mai muhimmanci magoya baya su riƙa ɗaukar abun ba ta ko a mutu ko a yi rai ba. Magoya bayan nan musamman talakawa kiran ya fi shafa da a ke batun su kan tura mota ta tashi ta bule da kura da barin su a tasha.

Wannan kuma bai nuna wanda bai yi nasara ba kar ya garzaya iya ƙarfinsa wajen shari’a don abi kadunsa. A baya mun ga waɗanda kotu ta soke zaɓe ta ba su nasara. A 2019 ma an yi abun mamaki inda ɓangarori biyu masu hamayya da juna na jam’iyyar APC a jihar Zamfara su ka shiga kotu.

Bangaren da bai amince da zaɓen fidda gwani ba ƙarƙashin Sanata Kabiru Marafa ne ya shigar da ƙarar inda Kotun Ƙoli ta yanke hukuncin ba a yi zaɓen fidda gwani na APC a Zamfara ba don haka a miqa ragama ga jam’iyya ta biyu mafi samun ƙuri’a.

Hakan ne ya kawo Bello Matawalle na PDP a wancan lokacin kan mulki. Kafin nan har zaɓaɓɓen gwamnan jihar na APC Shehu Mukhtar Kogunan Gusau ya fara shiryawa don karvar rantsuwar fara aikin da Allah ya hukunta ba zai fara ba.

Hukuncin kazalika ya kwavar da duk nasarar duk waxanda su ka lashe zaɓen majalisa a inuwar ta APC da hakan ya sa ’yan PDP su ka haye kujerun a bulus kuma bayan wani ɗan lokaci kuma Bello Matawalle ya fake da wani dalili ya sauya sheƙa zuwa APC sai ’yan majalisar su ka bi shi zuwa jam’iyya mai mulkin gwamnatin tarayya.

Ina ganin ɗan majalisa daya ne Kabiru Classic ya zauna a PDP amma shi kuma bai samu dawowa majalisar da za a kafa ta 10 a watan Yuni ba.

Aƙalla dai kowacce daga jam’iyyu masu tasiri sun samu aƙalla gwamnan jiha ɗaya. Yayin da zuwa yanzu APC ta fi yawan gwamnoni da ’yan majalisar taraiya, PDP ke bin ta a baya sai kuma NNPP ta samu lashe zaɓen babbar jihar Kano inda ita kuma Leba ta Peter Obi ta lashe zaɓen jihar Abia.

Idan an kammala sauran zaɓuka ko aiyana sauran kujeru za a kara fahimtar yadda takun siyasar 2023-2027 zai kasance. In za a tuna an gudanar da zaɓen jihohi 28 cikin 36 don sauran 8 din hukuncin kotu ya sauya lokacin zaɓensu daga na sauran dangi.

Zaben gwamnan Adamawa na neman raba kan mata da maza ’yan siyasa a Nijeriya:

Da alamu zaɓen gwamnan jihar Adamawa na neman raba kan mata da maza musamman ’yan siyasa a Nijeriya kan yadda lamarin ya shafi ɗaya ɓangaren.

A ra’ayin mata da dama zaɓen ’yar takarar APC a jihar zai buɗe dama ga mata su riqa tsayawa takarar manyan muƙamai kuma su na samun nasara.

Tun fara takarar, mata su ka taƙarƙare cewa a ba wa Binani goyon baya amma dalilan na kan gaba su ne kasancewar ta mace a ƙasar da maza su ka fi yawan kan madafun ikon siyasa.

A ɓangaren wasu ’yan siyasa maza ba duba mace ko namiji ya dace a yi ba. a’a wanda ya cancanta kuma ya lashe zaɓe da ƙuri’u masu rinjaye don mazan ma dai matan su ka haife su hakanan matan ma ’ya’yan iyaye maza ne.

Mataimakiyar shugabar mata ta APC a arewa maso Zainab Ibrahim na da yaƙini a ra’ayin ta cewa Aisha Binani ce ta lashe zaɓen da a ka ayyana a matsayin wanda bai kammala ba zuwa rubuta wannan shafi na ALƘIBLA.

Shi kuma jigon matasa a APC a Adamawa Idris Ahmed Tijjani ya karkata kan ji a ran sa cewa gwamnan jihar Umar Fintiri ne ya samu nasara kuma don buƙatar lumana ya dace a ba shi nasarar.

Ko da dai har zuwa rubuta wannan rahoto ba a samu mace da ta zama gwamna a Nijeriya ba, an samu mataimakan gwamna don ko yanzu ma ga Hadiza Balarabe a Kaduna da kuma ministar mata ta yanzu Pauline Tallen da ta taca zama mataimakiyar gwamna a Filato.

Wasu masu sharhin na karawa da cewa ko da za ka ga namiji a matsayin gwamna, to asalin gwamnar ta na gida don ba jihar da ba ofishin matar gwamna kuma da shawarar matan a ke tafiyar da mulkin jihohi a kan daidai ko akasin hakan.

Hukumar Zaɓen Nijeriya INEC ta bayyana cewa ta yi amfani da korafin manyan jam’iyyun hamayya wajen inganta zaɓen gwamnoni fiye da yadda ta gudanar da na shugaban ƙasa a watan jiya.

INEC ta ce fiye da kashi 90% na sauke sakamako ta hanyar na’urar BVAS ya yi aiki a zaven gwamnoni da na ’yan majalisar jiha duk da ma an kashe ɗaya daga jami’an hukumar.

Kwamishinan labaru da wayar da kan masu zaɓe na hukumar Festus Okoye ke magana bayan taron manema labaru ya na mai cewa a zaɓen na gwamnoni da ’yan majalisar jiha har jami’an zaɓe ke jiran masu kaɗa ƙuri’a su zo su kaɗa ƙuri’ar su kuma sauke alƙaluma a na’ura.

Ga kashe ɗaya daga ma’aikatan hukumar, Okoye bai ambaci jihar da hakan ya faru ba, ya na mai cewa za a fito da warin bayani amma wata ma’aikaciyar da a ka yi tsammanin ita ma an rutsa da ita daga bisani an gano ta na kwance a wani asibiti.

Okoye ya ce duk buƙatun da ’yan hamayya su ka bayyana a lokacin da dan takarar PDP Atiku Abubakar ya jagoranci zanga-zanga zuwa hukumar an shawo kan su a lokacin zaven jihohi.

Daga jihohin ɗan takarar NNPP a Yobe Alhaji Garba Umar ya ce zai gurfanar da INEC a gaban kotu don rashin sanya cikakkiyar alamar jam’iyyar sa a katin kaɗa wuri’a.

Shi kuma Idris Tijjani daga Adamawa ya ja hankalin hukumar zaven na tabbatar da ayyana ainhin wanda ya lashe zaɓen a jihar inda ya ce masu labarun yanar gizo na ruda jama’a.

A nan Okoye ya ce hukuamr na aiki don ’yan Nijeriya ne kuma ta na da ’yanci ba wai a ƙarƙashin wani ta ke ba.

“Kafin mu tafi zaɓe mu kan kira jama’a mu nuna mu su alamun da za a yi amfani da su na jam’iyyun su, su kuma amince kuma hakan mu ka aiwatar”

Da alamun dai iya abun da INEC za ta iya ambatawa kenan sauran ƙorafi kuma sai an gamu a kotu.

Kammalawa;

Akwai takaici ga wadanda su ka yi ganganci musamman wasu matasa a wasu jihohi da su ka rasa ran su a sanadiyyar neman sace akwatin zaɓe da kuma wasu dalilan daban. Haka kuma abun juyayi ne waɗanda wasu miygau su ka kashe don adawar siyasa.

In dai Allah ya kai mu za a rantsar da waɗanda su ka lashe zaɓe a ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa don haka fatan su cika alƙawuran kamfen za a yi don ka da a samu waxianda za ka kashe waya da sauya abokai bayan cimma burin su. Kazalika Allah ya ba wa waɗanda ba mamaki a ka zalunta a zaɓen nasara a kotu don hakan zai kara taimakawa wajen inganta zaɓe matuƙar kotu za ta zama mai sharewa wanda a ka cuta hawaye.

Mulkin dimokraɗiyya dai na da wa’adi ba kamar mulkin sarautar gargajiya ba ne. Don haka ko a na son wanda ya lashe ko ba a son sa wataran zai sauka kamar yadda shugaba Buhari ke nanata cewa ya kagara ya bar fadar Aso Rock.