EU za ta tallafawa gwamnatin Katsina da fam miliyan 10 domin samar da abinci mai gina jiki

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Sanarwa ɗauke da sa hannun babban sakataren yaɗa labarai na gwamna, Muhammad kaula ya sanar da haka ya kuma bayyana cewa Gwamna Dikko Raɗɗa ya samu yabo daga ƙasashen duniya saboda jagorancinsa wajen yaƙi da matsalar rashin abinci mai gina jiki a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya kuma koodinetan harkokin jin ƙai a Najeriya, Mista Mohamed Malick Fall, ya yaba wa Gwamna Raɗɗa a lokacin da ake gudanar da taron ƙolin da aka gudanar a Abuja mai taken “High-Level Conference on Mobilising Against Malnutrition.”

Koodinetan na MDD ya bayyana cewa fiye da yara miliyan uku ƙasa da shekaru biyar a Najeriya na fama da rashin abinci mai gina jiki mai tsanani, inda kusan miliyan biyu daga cikinsu ke jiran taimakon gaggawa.

Ya ce MDD da abokan haɗin gwiwa sun kai wa yara miliyan ɗaya magani, amma ya gargadi cewa jinkiri na nufin rasa makomar yara.

Mr, Fall ya roƙi gwamnonin yankin Arewa maso Yamma da su fitar da kuɗi, su shirya ƙungiyoyi, kuma su tallafa wa ma’aikata a cibiyoyin kula da lafiya, yana mai jaddada cewa akwai hanyoyin warware matsalar, kuma Najeriya na samar da kayayyakin abinci mai gina jiki.

Haka kuma, Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) ta bayar da alƙawarin tallafin fam miliyan £10m tare da ƙoƙarin haɗa ƙarin gudunmawa daga babban bankin duniya, shirin abinci na duniya (WFP), da ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa don taimakawa Jihar Katsina da dukkan yankin Arewa maso Yamma.

A jawabin sa, Gwamna Dikko Raɗɗa ya amince da cewa akwai matsalar rashin abinci mai gina jiki a jihar, tare da bayyana matakan da gwamnati ke ɗauka daga aikin noma don tabbatar da isasshen abinci, zuwa yaƙi da ‘yan fashi domin tabbatar da tsaron al’umma.

Dikko ya ce: “Mun amince da cewa muna cikin matsalar rashin abinci mai gina jiki, kuma dukkan ƙoƙarinmu sun nufi magance wannan matsala kai tsaye.”

Sakataren hukumar ci gaban Katsina (Katsina Development Management Board), Mustapha Shehu, ya bayyana taron a matsayin muhimmin mataki wajen kafa haɗin kai na gaskiya domin yaƙi da rashin abinci mai gina jiki.

Ya ce ƙungiyoyi da dama sun yi alƙawarin bayar da goyon baya wajen samar da abinci, magani da kuma inganta harkokin lafiya.

A jawabin rufewa, daraktar hanar na ƙungiyar Gwamnonin Arewa maso Yamma, Maryam Yahaya, ta bayyana sakamakon binciken Northwest Nutrition Survey 2024, inda ta ce kashi 16.6% na yara ƙasa da shekaru biyar a Jihar Sokoto na fama da rashin abinci mai gina jiki, kashi 11.6% a Katsina, da kashi 10.4% a Zamfara.

Ta bayyana cewa yara miliyan 2.8 a yankin na buƙatar taimakon gaggawa na abinci mai gina jiki, abin da ke nuna ƙaruwa da kashi 40% cikin shekara biyu.

“A Katsina, rabin yara masu ƙananan shekaru, ba su samun abinci mai gina jiki, wanda yasa basa sa mun ƙarfin jiki da zai basu damar yin karatu ko rayuwa cikin ƙoshin lafiya.”

Taron ya amince da a ƙaddamar da taswirar inganta abinci mai gina jiki ta Arewa maso Yamma (Northwest Nutrition Roadmap 2025–2028) — wacce za ta haɗa jihohi, abokan haɗin gwiwa, da bayanai cikin tsari guda.

An shirya taron ne ta haɗin gwiwar Gwamnatin Jihar Katsina da Médecins Sans Frontières (MSF), tare da goyon bayan Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU), UNICEF Nigeria, da sauran abokan ci gaba.

By ukarofi