Jami’ai sun rasu bayan ƴan bindiga sun farmaki ɗan Majalisar Wakilai a Neja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Majalisar Wakilai ta yi alla-wadai da mummunan harin ƴan bindiga akan tawagar motocin ɗan majalisa Hon. Jafaru Mohammed Ali da ke wakiltar mazaɓar Borgu/Agwara ta Jihar Neja, wanda ya yi sanadin rasa rayukan wasu daga cikin jami’an tsaron da aka wakilta don su ba shi kariya.

Rahotanni sun bayyana cewa al’amarin ya auku ne a ranar Laraba akan hanyar Lumma zuwa Babanna da ke Ƙaramar Hukumar Borgu, inda sanannen waje ne da ƴan bindiga ke addabar jama’arsa da kuma zirga-zirga su daga yankunan ƙasar Benin.

An farmaki ɗan majalisar da tawagarsa ne a lokacin da ya ke kan hanyar tafiya don ƙaddamar da wani aiki a mazaɓarsa, inda maharan da misalin karfe 1 zuwa 2 na rana suka buɗe wa motocin nasu wuta yayin da suke gab da isa ƙauyen Babanna.

A wata takarda da mai magana da yawun majalisar, Akin Rotimi ya fitar, ya tabbatar da cewa ƴan ta’addan sun halaka jami’ai da dama da raunata direban Hon. Ali da mataimakansa, lamarin da kuma ya yi sanadin farfashewar motoci masu yawa a sakamakon ruwan alburusai da suka sha.

Rotimi ya bayyana cewa, wajen da aka kai farmakin ya nuna cewa ƴan majalisa suna shiga yankuna masu hatsari domin tabbatar da amsa buƙatun al’ummominsu.

Ƴan majalisar sun kuma jaddada amfani da ikonsu na samar da dokoki wajen tallafa wa ayyukan daƙile ta’addanci da ke addabar al’umma a Neja da ma sauran jihohin Arewa.

Jihar Neja na fuskantar hare-haren ƴan ta’adda a ƴan watannin nan musamman a yankunan da ke kusanci da iyakoki masu hatsari.

By Babaji