Faɗan daba ya zama ‘gida-gida’ a Kano

Spread the love

Yadda al’amura suka dagule a unguwar Nasarawa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

A baya-bayan nan, ayyuykan daba sun sun mamaye lungu da saƙo na birnin Kano, Babban Birnin Jihar Kano, inda aka fara jin al’ummar jihar, musamman malamai, suna hawa munbari suna kiraye-kiraye kan batun.

A baya an fi samun rikicin a unguwannin talakawan birin kamar ɗorayi, Rijiyar Lemo, Birged, Fagge, ƙofar Nasarawa da dai makamantansu sun yi ƙaurin suna wajen guje-guje, saboda yadda ’yan daba kan faɗa wa mutane babu gaira babu dalili baya ga kashe mutane ta hanyar ƙwacen waya da ya yi ƙaurin suna.

Bugu da ƙari, al’ummar yankin Kawo da ke yankin ƙaramar hukumar Nasarawa a Jihar Kano sun shiga cikin fargaba mai tsanani bayan da rikicin da ake alaƙantawa da gungun matasa ya ci gaba har zuwa rana ta uku a jere, inda ya haifar da ruɗani da tsoro a tsakanin mazauna yankin.

Rahotanni sun bayyana cewa, rikicin ya dagula harkokin kasuwanci tare da hana walwala a hanyoyi, inda ’yan kasuwa, matafiya da mazauna gari suka shiga cikin yanayin tsoro da rashin tabbas. Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa lamarin ya zama kamar dawowar rikicin faɗan daba da ya daɗe yana zama barazana ga zaman lafiya a wasu sassan Kano. Wani mazaunin yankin mai suna Muhammad ya ce, rikicin ya tilasta wa ’yan kasuwa da dama rage harkokinsu saboda tsoron kai hari da fargabar rasa kaya. Ya ce, “Ba su kai hari cikin gidaje ba, amma suna tsoratar da ’yan kasuwa tare da kwace musu kaya a hanya.”

Rahotanni sun nuna cewa tushen rikicin na baya-bayan nan ya samo asali ne daga rigima tsakanin masu tuƙin adaidaita sahu da ta fara kusan makonni uku da suka gabata.

Wata mazauniya mai suna Mama ta bayyana cewa rikicin ya fara ne lokacin da wasu matasa suka tare babbar hanya da sassafe, suka hana wasu shiga hanyar. Ta ce, an nuna makamai a fili tare da yi wa abokan hamayya barazana, lamarin da ya janyo raunika da kuma lalacewar wani abin hawa.

Wani mazaunin yankin da ake kira Barrister ya ce rikicin ya haddasa cunkoson ababen hawa mai tsanani tare da jefa jama’a cikin firgici, duk da cewa ba a kai hari kai tsaye kan masu wucewa ba.

Wata mazauniya da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana halin da ake ciki a matsayin mai matuƙar tayar da hankali, inda ta yi kira ga hukumomi da su gaggauta shiga tsakani kafin rikicin ya ƙara taɓarɓarewa.

A nasa ɓangaren, wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Sagiru Yarima, ya danganta ƙaruwar rikicin da yawaitar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da kuma tasirin wasu ’yan siyasa a cikin harkokin matasa. Ya ce, rikicin gungun matasa ya ci gaba da yaɗuwa a cikin shekaru, inda wasu unguwanni a Kano suka zama cibiyoyin tashin hankali. Ya kuma nuna damuwa kan rahotannin amfani da bindigogi na ƙera gida, yana mai cewa hakan na ƙara barazana ga tsaron jama’a.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta bayyana cewa, tana sa ido kan halin da ake ciki tare da ƙara matakan tabbatar da tsaro a yankin da abin ya shafa. Rundunar ta ce, yawancin rikice-rikicen na faruwa ne tsakanin gungun matasa daga cikin al’umma guda, tana mai tabbatar wa jama’a cewa ana ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro don hana yaɗuwar rikicin. Haka kuma, rundunar ta ambaci kafa sabuwar sashen violent Crime Response Unit da aka horar musamman domin tunkarar manyan laifuka da rikice-rikicen matasa a jihar.

Duk da wannan tabbaci, mazauna yankin sun ce har yanzu suna cikin fargaba, yayin da ba a fitar da adadin waɗanda suka jikkata ko suka rasa rayukansu ba. Halin da ake ciki ya ƙara jawo kiraye-kirayen gaggawa ga hukumomin tsaro da shugabannin al’umma domin daƙile rikicin kafin ya rikiɗe zuwa babbar matsalar tsaro a jihar Kano.

By ukarofi

Leave a Reply