Fadar Vatican ta kori bishop bisa satar kuɗi da halartar gidan karuwai

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA, Abuja

Fadar Vatican ta sallami wani bishop ɗan ƙasar Amurka, Emanuel Hana Shaleta, bayan ya miƙa takardar murabus ɗinsa sakamakon zarge-zargen satar kuɗaɗe da kuma halartar wuraren karuwai a ƙasar Meɗico.

Rahotanni sun bayyana cewa an zargi bishop ɗin da satar sama da dala 250,000 daga kuɗaɗen cocin da yake jagoranta, tare da zargin cewa yana yawan zuwa wani gidan karuwai da ke Mexico.

Vatican ta sanar da amincewa da murabus ɗin nasa a ranar Talata, inda Paparoma Pope Leo XIV ya karɓi murabus ɗin daga muƙaminsa na jagorantar Eparchy of Saint Peter the Apostle of San Diego of the Chaldeans a Amurka.

A cikin wata sanarwa da Vatican ta fitar, ta ce: “Mai alfarma Paparoma ya amince da murabus ɗin Bishop Emanuel Hana Shaleta daga kula da eparchy na Saint Peter the Apostle of San Diego of the Chaldeans a Amurka.”

Rahotanni sun ce bishop ɗin ya miƙa takardar murabus ɗinsa tun a watan Janairu, kafin daga bisani hukumomi su kama shi.

An kama Shaleta ne a Filin Jirgin Sama na San Diego a ranar Juma’a yayin da yake ƙoƙarin tafiya zuwa Jamus, inda aka ce yana ɗauke da kusan dala 9,000 a tsabar kuɗi.

Kamen nasa ya biyo bayan wani rahoto da wani jami’in coci ya aikawa ofishin Sheriff na San Diego County tun a watan Agustan shekarar da ta gabata, wanda ya bayyana wasu zarge-zargen aikata ba daidai ba da bishop ɗin ke yi.

Daga bisani hukumomi suka gurfanar da shi a gaban kotu kan laifuka guda 15 da suka shafi badaƙalar kuɗaɗe, ciki har da almubazzaranci da kuɗi, ruf-da-ciki da kuɗaɗe da sauran laifukan tattalin arziki.

Sai dai bishop ɗin ya musanta dukkan zarge-zargen da ake yi masa lokacin da aka gurfanar da shi a kotu a ranar Litinin.

Rahotanni sun kuma nuna cewa masu bincike sun gano cewa an karkatar da kuɗaɗe daga wasu kadarorin cocin domin amfani da su wajen buƙatun kansa.

Binciken ya kuma nuna cewa an rasa aƙalla dala 427,000 daga kuɗaɗen cocin, yayin da wasu ke zargin cewa adadin kuɗaɗen da suka ɓace na iya kaiwa dala miliyan 1.

Bugu da ƙari, wani mai bincike mai zaman kansa ya gano cewa bishop ɗin na daga cikin mutanen da ke yawan zuwa Hong Kong Gentleman’s Club da ke yankin Zona Norte na Tijuana a Meɗico, wanda aka sani da cibiyar karuwanci.

Sai dai Shaleta ya dage cewa bai taɓa amfani da kuɗin cocin ba domin buƙatunsa na ƙashin kansa.

“Ina tabbatar da cewa ban taɓa amfani da ko sisi daga kuɗin cocin ba a duk rayuwata ta shugabanci a matsayin bishop. A maimakon haka, na yi ƙoƙari wajen kare da kuma sarrafa gudummawar da aka bayar ga coci,” inji shi.

By ukarofi