Birtaniya ta ƙaƙaba takunkumin samaniya da taƙaita zirga-zirga gabanin ziyarar Tinubu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA, Abuja

Gwamnatin ƙasar Birtaniya ta sanar da ƙaƙaba takunkumi kan sararin samaniya da wasu hanyoyi a garin Windsor gabanin ziyarar aiki da Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai kai ƙasar a mako mai zuwa.

’Yan sandan Thames Valley sun bayyana cewa, matakin na daga cikin tsauraran matakan tsaro da ake ɗauka, domin tabbatar da tsaron manyan baƙi a ƙasar, masu kallo da sauran jama’a yayin ziyarar Shugaban ƙasa Tinubu.

A cikin wata sanarwa, jami’in rundunar Thames Valley Police Joint Operations Unit, Chief Superintendent Adrian Hall, ya ce takunkumin sararin samaniya wani ɓangare ne kawai na manyan shirye-shiryen tsaro da aka tanada domin ziyarar.

Ya ce rundunar ‘yan sanda na da gogewa sosai wajen kula da manyan taruka na sarauta da ake gudanarwa a Windsor, don haka an ɗauki lokaci mai tsawo wajen tsara matakan tsaron da suka dace.

“Takunkumin sararin samaniya wani ɓangare ne kawai na tsauraran matakan tsaron da muka shirya domin ziyarar shugaban Nijeriya a mako mai zuwa. Akwai wasu matakan tsaro da jama’a za su gani, yayin da wasu kuma ba za su gani ba,” inji Hall.

Ya ƙara da cewa rundunar ‘yan sanda za ta tabbatar da tsaron dukkan mutanen da za su halarci ziyarar, ciki har da manyan baƙi, masu kallo da sauran jama’a, domin su samu damar shaida wannan muhimmin lamari cikin kwanciyar hankali.

Hall ya bayyana cewa Windsor Castle na da dokar taƙaita zirga-zirgar jiragen sama a sararin samaniyarsa a duk tsawon shekara, amma za a ƙara tsaurara wannan mataki a ranar 18 ga Maris domin inganta tsaro yayin ziyarar shugaban Nijeriya.

A cewarsa, takunkumin na wucin gadi zai fara aiki daga ƙarfe 7:00 na safe zuwa 11:59 na dare, tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Birtaniya (Civil Aviation Authority – CAA).

Matakan tsaron sun haɗa da taƙaita zirga-zirgar jiragen sama a sararin samaniyar yankin da kuma wasu takunkumi a kan hanyoyin mota, domin tabbatar da tsaro yayin ziyarar shugaban ƙasar Nijeriya.

By ukarofi