Sojoji sun ragargaza motocin yaƙin ’yan ta’adda a dajin Sambisa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF), ta kai wani farmaki ta sama cikin dajin Sambisa, inda ta lalata motocin yaƙi guda hudu tare da wasu muhimman kayayyakin aiki na ’yan ta’adda.

Rundunar sojin saman ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis, tana mai cewa an gudanar da harin ne a ranar Laraba, 11 ga Maris, 2026, bayan samun sahihan bayanan sirri da kuma sa ido na tsawon lokaci kan ayyukan ’yan ta’adda a yankin.

Daraktan Hulɗa da Jama’a da Watsa Labarai na rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce an aiwatar da harin cikin kwarewa, wanda ya haifar da kashe ’yan ta’adda da dama tare da raunana ƙarfinsu na ci gaba da kai hare-hare.

A cewarsa, wannan farmaki ya rage yawan damar motsi da kai farmaki da ’yan ta’addan ke da shi, tare da nuna irin tasirin amfani da bayanan sirri wajen gudanar da hare-haren soji na sama domin tallafa wa ƙoƙarin tsaro da ake yi a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya.

Harin na daga cikin ayyukan soji da ake gudanarwa ƙarƙashin Operation Haɗin Kai, shirin haɗin gwiwa na rundunonin tsaro da nufin murƙushe ’yan ta’adda da kuma dawo da zaman lafiya a yankin.

A wani ɓangare kuma, Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Kelɓin Aneke, ya sake jaddada ƙudirin rundunar na ci gaba da riƙe iko a sararin samaniya a wuraren da ake gudanar da yaƙi. Ya ce ci gaba da irin wannan iko na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da nasarorin da rundunonin tsaro ke samu a yaƙin da ake yi da ta’addanci.

Haka zalika, Mataimakin Babban Hafsan Ayyuka na rundunar, Air ɓice Marshal Precious Amadi, ya kai ziyarar aiki sansanin sojin sama da ke Maiduguri a jihar Borno, domin duba yadda jami’ai da kayan aiki ke shirye don ci gaba da gudanar da ayyukan soji.

A yayin ziyarar, an gabatar masa da cikakken bayani daga bangaren rundunar sama da kuma rundunar 105 Composite Group, wanda ya nuna irin shirin da sansanin ya ke da shi wajen ci gaba da gudanar da manyan ayyukan haɗin gwiwa tare da sauran hukumomin tsaro.

Haka kuma, Kwamandan Rundunar Sojin Sama ta Yankin Ayyukan Yaƙi (Tactical Air Command), Air ɓice Marshal MC Ekwueme, ya ziyarci sansanin, lamarin da rundunar ta ce ya ƙara ƙarfin gwiwar jami’an da ke aikin kare ƙasa a yankin.

Babban Hafsan Sojin Sama ya kuma jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da gudanar da hare-haren sama cikin tsari da haɗin gwiwa da rundunonin kasa domin takaita motsin ’yan ta’adda da kuma tabbatar da ɗorewar zaman lafiya a yankin.

By ukarofi