Daga AMINA YUSUF ALI
Barkanmu da sake haɗuwa a wani sabon makon a shafin zamantakewa a jaridarmu mai farin jini ta Blueprint Manhaja.
A wannan mako muna so mu warware yadda ake samun savanin fahimta tsakanin maza da mata a zamantakewa irin ta soyayya ko aure. Na san me karatu zai ce saɓanin fahimta?
Na’am saɓanin fahimta wacce ta ta’allaƙa a kan rashin fahimtar Yaren juna. Yare dai kamar yadda muka sani harshe ne kamar yarbanci ko Turanci ko Larabci da makamantansu. Kuma mai karatu ya san cewa da wuya mutane masu mabanbanta yaruka su iya fahimtar juna in dai kowa a cikinsu zai wa ɗanuwansa yaren da shi mai maganar ne kaɗai yake fahimta.
Don haka dole a samu fahimta yaren juna kafin a samu a isar da saqon da ake buƙata ya isa ɗin. Kamar yadda kuma muka sani, fahimta tana daga cikin jigon samun zaman lafiya a aure. Kuma samun zaman lafiya shi ne babban burin da ma’aurata suke so su cimma. Sai dai kash!
Ba kowanne gidan aure ake samun wannan fahimtar junan ba. Saboda kamar yadda wani mai bincike a ƙasar Turai ya bayyana, mata da maza sun zo daga Duniyoyi daban-daban ne. To kun ga Duniyoyi ma daban-daban ba ma yare daban-daban ba. Wasu lokuta akan samu rashin fahimta da isar da saƙo gamsasshe saboda wannan rashin fuskantar junan.
Me yake jawo saɓanin fahimtar?
Kamar yadda na yi muku shimfiɗa a baya, namiji da mace jinsuna ne mabanbanta waɗanda suka banbanta da juna a halayya da ɗabi’a da mu’amala da tunani da sauransu. A irin tunani na mace in dai ba shahshasha ba ce, duk lokacin da ta haɗu da namiji a zaman soyayya ko aure takan caje ƙwaƙwalwarta don ganin ta gano halayya da yanayin namijin dake tare da ita. Wata sai ta gane shi tsaf!
Wannan baiwa dai da ma ba kowacce mace ke da ita ba. Amma ma fi yawanci haka ne. Daga cikin dalilan da suka ba wa mace wannan dama har take fahimtar namiji shi ne, yawanci maza idan ba miskilaye aka samu na sosai ba, suna da bayyana halayyarsu ƙarara.
Sannan mace tana da ɗan zargi kaɗan da yake ba damar yin wasu zurfafan tunani; sannan abu na ƙarshe, namiji an san ya fi mace hankali, amma ta fi shi wayo. Wannan shi ya sa ta fi saurin gane ɗabi’a da ra’ayinsa fiye da yadda zai gano nata.
Kuma sannan tana gane saƙon da yake isarwa cikin ishara. Ita kuma mace ta fi isar da saƙonta cikin ishara. Ba ta fiye fitowa ta ce kaza take so ba ko wani abu. Ta fi son namiji ya gano me take so da kansa kuma ya yi mata wannan abun.
Idan ba a yi mata yadda take so ba, sai rigima ta tashi. Shi namiji sai ya rasa gane samanta da ƙasanta. Wasu lokutan ma sai ya harzuƙa a kan fushin da take yi. Domin shi har a zuciyarsa yana ganin bai ma yi wani abu ba. Yayin da ita kuma matar tasa gani take duk Duniya an ci zarafinta. Sai ka ga ta ƙullaci mijin a zo a yi ta takun saƙa a gidan. Wasu lokutan ma sai ta ji sonsa da kasashin kyautata mata ma ya fice a ranta.
Me ya sa ake so namiji ya fahimci yaren mace?
Wanan dole ne. Sanin Yaren abokiyar rayuwa yana da matuƙar muhimmanci a wajen namiji. Domin shi ne zai ba shi fahimtar juna da zaman lafiya a gidan aure. Zaman lafiya shi ne komai a gidan aure. Kuma duk gararambar namiji ba shi da inda ya fi gidansa muhimmanci a wajensa.
Yaya yaren macen yake?
Yaren mace shi ne a gano abinda take so a girmama shi a faranta mata rai da shi. Sannan a fahimci abubuwan da suke ɓata mata rai in dai ba sava wa addini ya yi ba, a guje shi, sannan a kula da ita. Shi ma sunnah ne. Manzon Allah SAW ya kasance mutum ma fi kyautata mu’amala da iyalansa. Me zai hana ku yi koyi da shi, Yayana?
Wasu daga cikin yarukan make masu wuyar fassaruwa wajen maza:
*Tana son ka dinga yi mata kyauta: Mace tana tsananin son mijinta ko saurayinta ya dinga yi mata kyauta. Ba wai don son abin Duniya ba ko wani abu ba. Mace tana alaƙanta kyauta da soyayya. Idan namiji ya yi mata kyauta komai ƙanƙantarta ta fi girmama fa fiye da ta kowa ko wacce ta saya da kuɗinta.
Da fatan ka gane wannan yaren Yayana. Idan kana yi wa budurwa ko bazawara kyauta alama ce a wajenta kana sonta kuma kai mutumin kirki ne ba da zancen wasa ka zo ba.
Akasin haka na zubar maka da mutunci a idon ta da na iyayenta. Ko da aure kuka yi, hakan abin yake. Kada ka ƙi yi mata kyauta don kana ciyar da ita da sauransu. Yi mata kyauta zai sa ta yi farin ciki kuma ku qara samun zaman lafiya a gidan aurenku.
Kulawa: Mace ko ba ta fito fili ta faɗa a, tana da tsananin jin yunwar kulawa. Ka nuna ka fahimci damuwarta. Rashin nuna mata haka zai sa ta ƙullace ka ta ƙi yi maka abinda zai faranta ranka.
Kai ma yadda ba ka ba ta kwanciyar hankali ba ta hana ka. Misali ‘yan ƙananan abubuwa da maza ke rainawa kamar ka kai ta unguwa a abin hawa ka, ko idan tana da ciki ta nuna tana kwaɗayin abu, kada ka nuna kawai shiririyarta ce, ka yi ƙoƙarin samowa inda hali.
Ko idan tana da wasu mutane masu muhimmanci a rayuwarta ka takura mata sai ta rabu da su ko nesanta mu’amala da su. Wata idan ta yi ƙoƙarin fahimtar da kai ka ƙi, to sai ta zuba maka ido. Amma za ta yi a ɓoye, sai dai za ta cigaba da tsanar ka da rashin ganin girmanka.
Idan kuma ka gane wannan karatun kuma ka aiwatar, sai ka ga nan da nan har alfahari take da kai ko wajen dangi da ƙawaye tana yaba maka ko da a bayan idanunka ne. Wannan kaɗan daga misalai kenan.
*Rarrashi da sauraro: Mace za ta yi ta gaya maka matsalolinta, wata kawai sauraro take so ka yi. Wata kuma tana so ka rarrashi ta ka ƙara mata ƙwarin gwiwa.
Misali, tana yi maka maganar yara suna ɓata kaya da yawa tana shan wahalar gyara. Wani namijin zai iya cewa to da me kuke yi idan ba za ki kula da su ba? Ko kin fiye lalaci.
Amma wanda ya fuskanci karatun zai iya kamo hannun ma ya duba tare da yaba mata ya ɗan rarrashe ta. Idan ta kama ma ya ce Allah ya hore masa arziki ya hutar da ita. Wannan yana ƙara qauna. Ƙauna tana sa zaman lafiya. Kuma a mintinan za ka aiwatar ba tare da ɓata lokaci ba.
*Lokacin fushi: Ya kamata maza su fahimci wannan yaren. mace idan tana cikin fushi ma rabin abubuwan da take faɗa ba a hayyaci take faɗarsu ba. Kuma ba wai yana nufinsu har zuciyarta ba.
Misali mace idan kana wani hali wanda ta bi duk wasu hanyoyi ka qi rainawa za ta iya cewa, kawai ka sake ta ta huta, ko wani abu. Duk da dai ita ma bai kamata ta faɗa ba. Idan ya vaci bai kamata idanun su rufe ba. A kama baki, zazzafan fushi daga ibilis la’ananne yake.
To kai ma miji ya kamata ka fahimci haka kada kai ma fushi da girman kai su azalzala ka ka aikata abinda za ka yi nadama. Mace mai irin wannan nasiha take buqata ko kuma ka ɗauki mataki horas da ita a shari’ance ko ka haɗa ta da waliyyanta.
- Fahimtar buƙatunta: Yayin da wasu matan kan buɗe baki su bayyana maka buƙatunsu, wasu matan ba sa iyawa saboda kunya ko wasu dalilai. Idan mace na buƙatar kuɗin wajen namiji wata ta dinga zagaye-zagaye.
Da ma Yayana idan ka ga an fara zagaye-zagayen nan, to ka ɗau haske kawai. Ba sai an yi maka ɓaro-ɓaro ba. Haka idan mace na buƙatar kulawar namiji a shimfiɗa za ka ga ita ma wata sai dai ta yi shiga mai jan hankali, ko ta ɗan zauna kusa da shi, ko ta ɗora masa hannu ko ƙafa. Kai Yayana daga an yi haka a dinga ɗaukar haske.
Shi namiji a yarensa gani yake shi kaɗai ke da buƙatar saduwa don haka sai lokacin da yake buƙata zai kusanci iyali. Shi ya sa wasu matan suke amfani da jima’i don wahalar da maza musamman masu mata guda. To ka ji yaren nan, ita ma tana buƙata kamar ka. Kawai dai ba za ta fito ta bayyana ba ne a kowanne lokaci.
- Ba ta lokaci: Shi namiji yana ganin ba wa mace lokacinsa ba wani abu ne mai muhimmanci ba. Sau da yawa mace za ta kira namiji ko ta yi masa saqon tes ya ƙi ba ta amsa. Shi a ganinsa ba wani abu ba ne, za ta fahimci aiki ne ya yi yawa.
Amma a wajen mace, wannan babban savo ne da zai iya sa ta ta shiga mawuyacin hali a zaman aure ko soyayya. Wata ma yanke hukunci za ta yi na zargi wai ba ka sonta, ko kuma kana da wacce kake kulawa ka manta da ita.
Kai ma Yayana idan za ka tuna ai kafin ta shigo hannu ba haka kake mata ba. Waccan tsohuwar hanyar da kake samun lokaci ka yi mata waya da tes shi za ka nema ka cigaba ko da bai kai na da can ba.
*Ƙaurace mata shi ma yana isar da saƙo kala-kala a zuciyarta. Za ta yi ta saɗe-saƙe tana ƙoƙarin neman dalili. Idan wani dalili ko lalura ce ta sa ba ka kusantarta sosai, sai ka zaunar da ita ka fahimtar da ita matsalar idan mai fahimta ce. Idan ma ba za ta fahimci gaskiyar ba, yi mata ‘yan dabaru. Ko musulunci bai hana a yi ‘yar ƙarya don a zauna lafiya, sai dai idan mutum kada ya wuce ta zama ɗabi’arsa
A inda gizo yake saƙar:
A inda gizo yake saƙar shi ne maza na ganin ɓata lokaci ne su dage sai sun fahimci ɗabi’ar mace ko yaren da take fahimta. Amma a zahirin gaskiya dole ne.
Domin mace ita ce mahaifiyarsa ko ‘yarsa ko matarsa su ne makusantanka fiye da kowa. Sai dai haƙƙin kowacce ya banbnta daga wata zuwa wata. Sanin yaren mace zai taimake ka ka fahimci mahaifiyarka wacce take da alaƙa da gamawa da lafiyarka ko akasin haka.
Sanin yaren mace zai taimaka maka ka zauna lafiya da matarka wacce ta kasance cikon addininsa kuma cikin farin cikinsa. Duk inda zai je dole ya dawo gida. Kuma yadda ya shimfiɗa gidan haka zai tarar da shi. Sanin yaren mace zai sa ka san yadda za ka faranta mata. Kuma idan mace tana cikin farin ciki a gidan aure, to ka gama samun nasara ta zaman lafiya.
Sa ta farin ciki zai sanya yarda a tsakaninku ta yadda za ka mulke ta cikin sauƙi. Mace idan ta yarda da kai tana sakar maka linzaminta ka juya ka karya yadda kake so. Mace raƙumi takan zama raƙumi da akala ga wanda ya nuna tausayinta ya girmama ta. Mu haɗu a wani makon idan Allah ya kai rai.
