‘Yan sanda sun gargaɗi masu yin fim da ke amfani da kayansu ba tare da izini ba

Daga AISHA ASAS

Hukumar ‘yan sanda ta ƙasa ta nuna damuwarta kan yawaitar amfani da kuma mallakar unifom ɗinta da wasu daga cikin kayan aikinta ba tare da amincewarta ba, wanda wasu masu shirya finafinai ke yi.

Hakazalika ta koka kan yadda ake siyar da kayan aikin nata a shaguna da kuma hannun ‘yan kasuwa waɗanda hukumar ba ta ba su izinin yin hakan ba.

Sufeto Janarar na ‘yan sanda ya nuna fushinsa kan wannna wulaƙanta kaki da kuma aikin na ɗan sanda da masu shirya finafinai ke yi. Ya kuma nuna rashin dacewar abinda suke yi da kuma sava wa doka ta sashi na 251 na dokar ‘Criminal Code’ da kuma sashi na 133 na dokar ‘Penal Code’.

An bayyana hakan ne a wani taro na manema labarai da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar, ya bayyana cewa, Sufeto Janarar ya bayar da umurnin gaggauta kame da hukuntawa daidai da yadda doka ta tanadar ga mutanen da ke siyar da kayan aikin ‘yan sanda ba tare da neman izini ba.

Kazalika ya yi kira da babbar murya ga masu shirin fim da ke nuna ɓatanci ga jami’an tsaro na ‘yan sanda a finafinan su ba tare da sun nemi izinin yin hakan ba, da su gaggauta dainawa ko su fuskanci fushin hukuma.

IG ya ƙara da tabbatar da cewa, hukumar ‘yan sanda zata dage wurin ganin an bi doka kuma an yi hukunci daidai da yadda dokar ƙasa ta tanada. Ya kuma bayyana wannan doka ta hana amfani da kayan ‘yan sanda ba tare da neman izini ba a matsayin hanya ta tsaftace aikin nasu.

Sannan ya tabbatarwa masu buƙatar amfani da su a shirin fim, ko nuna wani abu da ya shafi aikin ɗan sanda cewa, rundunar ‘yan sanda za ta ba su goyon baya ɗari bisa ɗari a lokacin da suka zo neman izinin, wanda aka ɗora alhakin hakan a ofishin Jami’in Hulɗa da Jama’a.