Rarara ya shirya taron addu’a kan matsalar tsaro

Daga AISHA ASAS

Matsalar tsaro ta zama babban abin da ke ci wa ‘yan Arewa tuwo a ƙwarya, kuma ya zama silar da ya hana cigaba tare da walwalar mutanen da ke cikinta. Kasancewar ta zama cutar da ta ƙi jin magani, ta ƙi ci, bare har ta kai ga cinyewa, ya sanya duk wani mai kishin Arewa shiga nazari da dogon tunani kan hanyar da zai iya taimaka wa cibiyar tasa don ganin an kawo ƙarshen wannan kisan ƙilla da azabtarwar da ake yi wa ‘yan’uwa mazauna wannan yanki da suka faɗa hannun mutanen da ke jan ragamar wannna ta’adanci.

Dauda Kahutu Rarara, shugaban ƙungiyar 13×13, kuma shararren mawaƙin siyasa na Jam’iyyar APC, ya bi jerin ‘yan Arewa masu nema wa yankin nasu mafita kan matsalar tsaro, ta hanyar shirya taron addu’a ta musamman kan sha’ani na rashin tsaro, don neman taimakon Mai Ƙarfin iko, masani sirri da bayyane, kan wannan mawuyacin hali da Arewa ta samu kanta a ciki.

Mawaqin ya bayyana cewa, wannann taro ba na ƙungiyar 13×13 ne kawai ba, domin taro ne da ya haɗa masu faɗakarwa wato ‘yan fim da kuma alarammomi irinsa, don nema wa Arewa mafita wurin wanda yake da abin bayarwa. Ta hanyar karanta Alƙur’ani mai tsarki da addu’oi na newa wa Arewa sauqi daga halin da ta riske kanta.

“Dama ita ƙungiyar 13×13 aikinta ta hankaltar da al’umma kan abin da ya kamata ta yi a neman mafita. Kuma harkar fim da waƙa ba wata hanya da ta kaita son zaman lafiya,” in ji shi.

Ya kuma bayyana wannan taro a matsayin ta su hanya ta nuna damuwa da kuma fara aikata abinda ya kamata, wanda suke fatan wasu su biyo baya. “Fatanmu mutane su miƙe, gida-gida da Masallatai a dage da addu’a, domin samun sauƙin halin da mu ke ciki.”

Da yake amsa tambayar manema labarai kan zargin haɗa wannan taro don tallata ɗan takaransa wato Ahmad Bola Tunbu, wato dai rufe kura da fatar akuya, mawaɗin ya ce, “wannan dai watakila kai kake tunanin hakan, domin dai a yanzu mu tunanin da mu ke yi na ƙasa ne ba wai siyasa ko ɗan takara ba.

Domin idan ana zance na ƙasa, to fa sai an samu abinda zai raya ƙasar ne tukuna su masu mulkin za su samu damar yin mulkin. Zaman lafiyar ƙasar nan shi ne zai taimaki duk wata siyasa da za a yi a ƙasar nan.

Wannan zance ne na haƙƙin da ya rataya kanmu, mu ‘yan ƙasa, domin idan har Shugaban Ƙasa zai yi nasa, jami’an tsaro su yi na su, to fa mu ma ‘yan ƙasa ya kamata mu yi namu. Magidanci ma da yake shi da matarsa, akwai rawar da zai iya takawa. Saboda haka dukkanmu sai mun haɗu, mun taimaka da bayyanai da bin dokokin da jami’an tsaro suke saka mana. Don ganin mun ga ƙarshen wannan al’amari.”

Rarara ya kuma ƙara da bayyana muhimmancin abinda aka yi a zaman taron wanda shine karatun Alƙur’ani mai tsarki, wanda yake da matuƙar banbanci da saka waƙar ‘Jagaba shine gaba’, hakan zai ba wa mai zargi amsar tambayarsa.

Shugaban na ƙungiyar ta 13×13 ya ƙara da bayyana kansu a matsayin abin koyi da ɗimbin mutane suke bibiya da kwaikwayon abinda suka yi, hakan zai taimaka matuƙa wurin raja’ar mutane ga neman tallafi daga wurin Mahallici, a ƙoƙarinsu na koyi da waɗanda suke so wato su.

Ya kuma janyo hankalin mutane ga sanin muhimmancin littafi mai tsarki wato Alƙur’ani, wanda ya bayyana a matsayin ƙoramar ilimi kuma maganin kowacce matsala ta duniya. Ganin muhimmancin hakan ne ya sa suka gayyato dattijai daga cikinsu, domin su zauna, su bada gudunmawa kan wannan matsala ta tsaro, kuma su ilimintar da al’aumma kan abinda ya dace su yi a irin wannan lokaci na tashin hankula.

Rarara

A ɓangare ɗaya, Rarara ya taɓo zancen takwarorinsu na Kudu wato ‘yan wasan Nollywood da tsautsayi ya jefa su hannun ‘yan garkuwa da mutane. Ya bayyana irin tsarin da gwamnatin Arewa musamman Kano ta yi kan harkar fim a irin wannnan yanayi na rashin tsaro.

“A nan Kano dai idan za ka yi fim a yanzu, akwai takardar da ake ba ka, wadda za a sanar da jami’an tsaro, za su san a inda za ka yi aikin naka. Ko da ba za su zo wurin ba, za su riƙa zagayowa, ko da wani abu zai faru, sun san da zuwan naka.”

Daga ƙarshe ya yi kira ga mutane da su tashi su nemi katin zaɓensu, don ganin sun zaɓi wanda zai iya kawo masu cigaban da zai hana su zaman banza, wanda shine ƙashin baya na duk wata matsala ta tsaro da Arewa ke fama da ita.

“Duk fa wanda wannan matsala ta rashin tsaro ta dame shi to ya kamata matsalar rashin aikin yi ta dame shi, domin ita ce ta janyo wannan. Misali, duk wani ɗan jarida da ya zo nan wurin daga fa wurin aikinsa ya fito, to ina ya ga lokacin da zai zauna da wannan ya zauna da wancan har a kai ga haɗa wani abu da ba daidai ba. Sai dai idan abin alkhairi ne ko na samu, za ka ga sun haɗu don cigaban aikinsu ko kansu.”