Yaron da ya yi bulaguro zuwa waje zai koma gida

Daga BELLO WANG

A kwanakin nan, maganar Taiwan ta sake janyo hankalin mutanen duniya, sakamakon yadda wata babbar jami’ar ƙasar Amurka ta kai ziyara a yankin Taiwan na ƙasar Sin, duk da rashin amincewa da gargaɗi da gwamnatin ƙasar Sin ta yi, lamarin da ya tilasta wa Sin daukar wasu matakai, ciki har da atisayen soja a kewayen tsibirin Taiwan.

Duk lokacin da aka ambaci Taiwan ya kan sa ni tunawa da wani batun da ya faru a baya: Wata rana, na je ajiye kudi a wani banki a birnin Ikko na Najeriya.

Ina jira a zo kaina, sai wani ma’aikacin banki ya taimaye ni, “Me ya sa ƙasar Sin ba ta yarda da ‘yancin kan Taiwan ba?”. Maimakon na amsa tambayarsa, sai ni ma na yi masa tambaya:

“Me ya sa Najeriya ba ta yarda da ‘yancin kan Biafra ba?” Ma’aikacin ya rasa abin da zai fada.

Wasu kafofin yada labaru da ‘yan siyasa na ƙasashen yamma suna son kwatanta Taiwan da Ukraine, amma haƙiƙa akwai bambanci tsakaninsu. Ukraine wata ƙasa ce, yayin da Taiwan wani yanki ne na ƙasar Sin. Ƙasar Sin ba za ta yarda da ‘yancin kan Taiwan ba, kamar yadda ita ma gwamnatin Najeriya ba za ta taba amincewa da ɓallewar yankin Kudu maso gabashin kasar, da kafuwar “jamhuriyar Biafra” ba.

Duk wanda ya ke karanta labarun abubuwan dake faruwa a sassan duniya, tabbas ya taɓa jin manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya. Ma’anar wannan manufa ita ce:

Ƙasar Sin ɗaya ce tak a duniyarmu, Taiwan wani yanki ne na ƙasar Sin da ba za a iya balle shi ba, kana gwamnatin jamhuriyar jama’ar ƙasar Sin, ita ce halaltacciyar gwamnati ɗaya tak da take wakiltar ɗaukacin al’ummun Sin. Wannan manufa ita ce tushen ƙulla hulɗar diplomasiya tare da ƙasar Sin, kana wata babbar ƙa’ida ce da Majalisar Ɗinkin Duniya da gamayyar ƙasa da ƙasa suke amincewa da ita.

Saboda dukkan ƙasashen da suka ƙulla huldar diplomasiya tare da ƙasar Sin sun yin alkawarin girmama manufar kasancewar ƙasar Sin ɗaya tak, sa’an nan galibin ƙasashen duniya sun riga sun ƙulla hulɗa da Sin.

Don haka, idan kowace ƙasa ta iya cika alƙawarin da ta yi, to, ba za a samu maganar Taiwan ba. Amma abin takaici shi ne, akwai ƙasar da ta yi amai ta lashe kan wannan manufa.

Babban dalilin da ya haddasa maganar Taiwan shi ne ƙasar Amurka. Da ma a shekarar 1949, Sinawa sun kawo karshen yakin basasa na ƙasar na shekaru 3, tare da kafa jamhuriyar jama’ar kasar Sin.

A lokacin, wasu sojoji da jami’ai na jam’iyyar Kuomintang sun gudu zuwa tsibirin Taiwan na ƙasar, inda suka mallaki tsibirin bisa goyon bayan gwamnatin ƙasar Amurka. Daga bisani, Amurka ta fara yin amfani da maganar Taiwan wajen neman shawo kan ƙasar Sin:

Idan tana neman samun goyon bayan ƙasar Sin, sai ta dan nisanta kanta da ɓangaren Taiwan. Amma idan tana so ta matsawa kasar Sin lamba, to, sai ta bijiro da maganar baiwa yankin Taiwan tallafin makamai, da nuna goyon baya ga masu neman ‘yancin kan Taiwan a asirce, ko kuma sanya wasu manyan jami’anta kai ziyara yankin Taiwan, da dai sauransu.

Sanin kowa ne cewa, Amurka ta kwashe fiye da shekaru 70 tana yin haka, shin za ta iya kiyaye yanayin a wannan zamanin da muke ciki? Bayan da Nancy Pelosi, babbar jami’a mai matsayi na uku a gwamnatin ƙasar Amurka, ta ziyarci yankin Taiwan a wannan karo, rundunar sojojin ƙasar Sin ta ƙaddamar da babban atisayen soja a kewayen Taiwan, wanda ba a taba ganin irinsa ba a baya.

Hakan ya shaida ƙarfin ƙasar a fannin dinke kasa ta matakan soja. Sai dai za ta ci gaba da neman dinkuwar ƙasa waje guda ta hanyar lumana. Sinawa suna da cikakken imani kan makomar lamarin.

A ganinsu, abin da ya faru sakamakon yadda al’ummar kasar ba su da ƙarfi a baya, za a iya daidaita shi, bayan da ƙasar ta samu ci gaba, da farfaɗowar al’ummarta.

A ganin Sinawa, yankin Taiwan tamkar wani yaro da ya bar gida, ya tafi bulaguro a waje, kuma tabbas wata rana zai koma gida.