Fa’idojin cire tallafin man fetur guda biyar – Masana

Daga AMINA YUSUF ALI

A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne fai shugaban ƙasar Nijeriya Bola Tinubu ya ba da sanarwar cire tallafin man fetur jim kaɗan bayan rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasar. Wato babu kasonsa a cikin kasafin kuɗi bayan wannan sabon wata da ya kama na Yuni.

Shi tallafin man fetur wani tallafi ne daga gwamnati wanda take ba w atalaka, don rage masa tsadar man fetur. Don ya samu sauƙin farashin sayen man.

Talakawa sun tashi hankalinsu matuƙa game da wannan cire tallafin domin ana ganin talakan zai iya shiga matsin tattalin arziki da talauci sakamakon haka.

Amma a wani sakamakon bincike da masana tattalin arziki suka yi a kan wasu fa’idoji guda biyar na cire tallafin mai. Kamar yadda jaridar Ingilishi ta The Nation ta wallafa.

  1. Cire tallafin zai sa a samu wasu kayayyakin da suke a voye su wadata.
  2. Gwamnati za ta samu rangwame a kan kuɗin da take kashewa wajen cikin tallafin man fetur ɗin. Gara a yi amfani da kuɗin wajen harkar ilimi, lafiya, kayan more rayuwa, da sauransu.
  3. Zai ba da damar samar da matatun mai na cikin gida don samar da qarin man fetur da dangoginsa. Kuma hakan zai rage wa Nijeriya dogaro da man fetur da aka shigo da shi daga waje.
  4. Samun isassun matatun mai a ƙasar Nijeriya za au bunƙasa tattalin arzikin ƙasar.
  5. Yawan matatun mai a ƙasar zai samar da guraben aiki birjika ga ‘yan Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *