Falalar yin sallar Asham

Assalamu alaikum, da fatan kowa yana lafiya, Allah ya haɗa mu da alkhairan da ke cikin wannan wata mai albarka ta Ramadan, Allah ya albarkaci jaridar Blueprint Manhaja.

Kamar dai muka sani ne cewa, wannan wata ta ibada ce. A cikin falalar yin sallar Asham a cikin wata Ramadan, wanda ya yi Asham a dare na farko a watan Ramadan Mumini yana fita daga cikin laifinsa kamar yadda mahaifiyarsa ta haifeshi.

•Wanda ya yi Asham a dare na 2 Allah zai gafartawa iyayansa.

•Wanda ya yi Asham a dare na 3 wani Mala’ika zai kira sunansa a ƙarƙashin al’arshi ya ce a nunka ayyukan Alkhairi kuma a gafarta laifukansa.

•Wanda ya yi Asham a dare na 4 za a ba shi ladan wanda ya karanta Attaura, Injila, zabura, da Alƙur’ani.

•Wanda ya yi Asham a dare na 5 za a ba shi ladan ya yi sallah a makka da Madina.

•Wanda ya yi Asham Adare na 6 za a ba shi ladan mala’ikun da su ke kewaye da Baitul ma’amuri kuma dukkan dutse da marmara za su nemi a gafarta masa laifukansa.

•Wanda ya yi Asham a dare na 7 kamar ya riski Annabi Musa ne ya taimake shi a kashe Fir’auna da Hamana.

•Wanda ya yi a dare na 8 Allah zai ba shi ladan da ya bai wa Annabi Ibrahim.

•Wanda ya yi a dare na 9 kamar ya bautawa Allah ne irin wanda Annabi Muhd (SAW) ya yi wa Allah.

•Wanda ya yi a dare na 10 Allah zai azurta shi da alkhairan duniya da lahira.

•Wanda ya yi a dare na 11 zai fita daga duniya kamar yadda aka haife shi.

•Wanda ya yi a dare na 12 zai zo ranar alƙiya yana amintacce.

•Wanda ya yi a dare na 13 Allah zai gina masa birni a gidan Aljanna.

•Wanda ya yi a dare na 14 Mala’iku za su zo su yi masa shaidar ya yi sallar Asham ba za a yi masa hisabiba.

•Wanda ya yi a dare na 15 Mala’iku za su yi masa salati da maɗauka Aa’arshi da kursiyu.

•Wanda ya yi a dare na 16 Allah zai rubuta sunansa daga masu kuɓuta daga wuta.

•Wanda ya yi a dare na 17 za a ba shi lada kamarna dukkan Annabawa.

•Wanda ya yi a dare na 18 wani mala’ika zai kiransa ya ce ya kai bawan Allah, Allah ya yarda da kai da mahaifanka.

•Wanda ya yi a dare na 19 Allah zai ɗaga matsayinsa a Aljanna Firdausi.
Ya Allah ka ba mu rabo duniya da lahira.

Saƙo daga Umar Yahaya Bello, 08133114144.