Rayuwar Michael Jackson, sarkin gambarar zamani

Daga AISHA ASAS

Ba-Amurken mawaƙi da duniya ta sani kuma ta ke bibiyar sa fiye da kowanne mawaƙi da tarihi ya san da zamansa. Ya kafa tarihin da ake tsammanin ba a nan kusa ba samun wanda zai iya kai inda ya kai bare har ya fi shi. Mawaƙi ne da ke waƙa daidai da zukatan mutane mafi rinjaye masu muradin kaɗe-kaɗe, kai har ma waɗanda ke ƙoƙarin ganin ba su bi hanyar da rawa da waƙa ta bi wasu daga cikin su na ganin ƙwarewarsa.

Michael Joseph Jackson, sarkin gambarar zamani wato ‘King of hip pop’ a Turance, ya kasance matashin da ya shiga duniyar waƙa cikin ƙurciyarsa, kuma ya shiga da ƙafar da ta fi ta matasa ‘yan’uwansu. Matashin ya samu karɓuwa tun a ƙarni na 20, jim kaɗan bayan fara haskashi a matsayin mawaƙi.

Duk da cewa, duniyar waƙa ta nahiyar Turai ta ƙyanƙyashe zaratan mawaƙa da suka cancanci jinjina, kamar, Elvis Presley da kuma Paul McCarthy, waɗanda nahiyar Turai ta girgiza da amon sautinsu. Sai dai sun kasance mawaqa da suka sace zukatan nahiyar ta Turai kawai, ciki kuwa har da shi Michael Jackson, domin ya bayyana burinsa na taka inda suka taka a duniyar waƙa, a lokacin da yake tasowa kenan.

Michael Jackson

Shi kuwa ya zama zakaran gwajin dafi ne saboda ya haɗa nayihar Turai da wasu ɓangarori na duniya, hakan ya sa ƙuri’un masoyansa suka yi wa na su zarra.

Wannan bai rasa nasaba da cewar da ake yi amon gangarsa na tafiya daidai da al’adun mutane da dama a faɗin duniya. Idan kuwa ka kwatanta, zai yi wahala ka rasa wata waƙa da kiɗanta ya yi kamanceceniya da kiɗan al’adarka.

Wannan dalilin ne wasu ke cewa, shine Dujjal ɗin da aka faɗa zai zo a ƙarshen duniya, ya ja mabiyansa zuwa wuta. A cewarsu, shi Dujjal ɗin zai zo da ganga, yana kiɗa, duk wanda ya bi shi, zai samu kansa a wuta.

Kada ku tambaye ni sahihancin wannan fassarar ta su ta abin da Dujjal ya siffantu da shi, domin ban san inda suka samo ba.

Zancen a nan shine, Michael ya yi shaharar da duniya ba ta taɓa gani ba, wannan ce ta sa ake ganin shi a matsayin abin da ya wuce baiwar ɗan Adam, sai dai wata ishara ko cika umurnin wanda ya halicci ɗan Adam.

Shin wane ne Michael Joseph Jackson?
Michael Joseph Jackson ɗan Ƙasar Amurka, daga Gary, Indiyana. An haife shi a ranar 29 ga watan Agusta, 1958. Michael ɗa ne na takwas a wurin mahaifinsa Joe ko kuma Joseph Jackson, yayin da ya zamo yaya ga ƙanne biyu, a taƙaice su goma ne mahaifin na su ya yi sanadin zuwansu duniya. 

Tare da mahaifiyarsa

Michael ya fara shiga harkar waƙa ne a shekara ta 1967 tare da ‘yan’uwansa; Jackie, Tito, Jermaine da kuma Marlon, a matsayin ‘Jackson 5’ wanda daga baya aka sauya wa suna zuwa ‘The Jacksons’.

A shekara ta 1971, Michael ya fita daga cikin ayarin mawaƙan ‘The Jacksons’ don fara waƙa ta karan kan sa tare da shahararren kamfanin waƙa na ‘Motown Records’. A shekara ta 1979 ne ya zama mawaƙi mai zaman kan sa, inda ya fitar da albom ɗinsa na ‘Off the Wall’. 

Fita daga cikin ayarin ‘yan’uwansa da Michael ya yi ba zai rasa nasaba da cin zarafin da mahaifinsa yake masa lokuta da dama ba. Domin ba sau ɗaya ba, mawaƙin ya sha bayyana wa a wasu daga cikin tattaunawar da ake yi da shi cewa, mahaifinsa na cin zarafinsa na fili da na ɓoye, wato dai duka da zagi. Ba zan manta ba, a wata tattaunawa, yayin da yake ƙoƙarin amsa tambayar dalilin da ya sa ya yi canjin yanayin fuska, ma’ana tiyata ta gyara fasalin fuska wato ‘plastic surgery’, a cikin ɗaya daga cikin bayyanan na sa, mawaƙin ya bayyana cewa, mahaifinsa na yawan zagin hancinsa, inda a kullum yake kiransa da mai ƙaton hanci. Wannan na ɗaya daga cikin dalilan da ya sa shi sauya fasalin fuskar, ciki kuwa har da hancin na sa da ya dawo daidai da irin na mahifiyarsa, wadda ƙanwarsa da ya kwaikwayi fuskar ta ta, wato Janet Jackson ta ke da irin sa.

A ɓangaren barin ‘yan’uwansa kuwa, ya samo asali ne tun daga tushen kafuwar mawaƙan, domin mahaifin na su wanda ya kasance tsohon ɗan dambe ne,shine jagoran tafiyar ta su ta ‘The Jacksons’, don haka ya fuskanci matsaloli a zaman na sa da shi, ciki kuwa har da duka da zagi a yayin bita.

Duk da cewa, Michael ba shi ne kaɗai yaro a gidan da ya fuskanci ƙuncin rayuwa daga mahaifin na su ba, sai dai ga dukkan alama na Michael ɗin na musanman ne, domin duk ya fi su abin faɗa. Kuma wannan rayuwar da ya yi da mahaifin na sa ta rayu har zuwa ƙarshen rayuwarsa, domin an tabbatar da bai sanya mahaifin na sa a gadonsa ba, ma’ana ya haramta wa mahaifinsa cin ko ficika daga cikin abin da ya tara bayan mutuwarsa. Duk da cewa, a zantawarsa da Oprah, kafin mutuwarsa, ya bayyana yafiyarsa ga mahaifin na sa.

Mahaifiyarsa wadda bayyanai suka tabbatar da ita a matsayin uwa ta gari ga ‘ya’yanta ta hanyar nuna masu so da kulawa, kuma ita ce silar baiwar waƙa da suke da, wato dai sun gaji wani ɓangare na duniyar waƙa daga wurinta, domin cikin ayyukan da ta yi a ƙoƙarin ganin ta saka abinci a bakunan ‘ya’yanta akwai kiɗa na piano da kuma wasu nau’ukan ganga. Duk da cewa ba za a ce mahaifiyar su suka gada ba kai tsaye, domin mahaifin na su ma na da na sa baiwar, duk da ba za a iya kiranta ta waƙa kai tsaye ba, domin ta sa baiwar ta iya taimakon masu baiwar ne don ganin sun zamo abin da ake so da sha’awar saurare. A taqaice dai baiwar waƙa ba a ƙasa Michael ya tsinta ba.

Baiwar Michael ba ta tsaya iya rera waqa ba ne, domin ya kasance marubucin waƙoƙi, na sa da na wasu da suka yi shuhura, kuma ɗan rawa ne da har ta kai ya ƙyanƙyashe wasu daga cikin sanannun nau’ukan rawa da duniya ta sani kuma take amfani da su, misali, rawar da ake yi wa suna da ‘moonwalk’ da sauransu. ma’ana dai ya haɗa duk wata baiwa da duniyar waƙa ta ke buƙata don kammaluwa.

A ranar 25 ga watan Yuni, shekara ta 2009 ne duniya ta yi rashin mawaqi ɗan baiwa Micheal Jackson, cikin Ƙasar Amurka ya cika, Los Angeles. Bai mutu ba har sai da ya auri mata biyu, waɗanda aka ce ya yi auren sharaɗi ne da su wato ‘contract marriage’ a Turance. 

Mahaifin Michael Jackson

Ta farkon ta kasance ‘ya ga shahararren mawaƙin nahiyar Turai wato Elvis Presley, mai suna Lisa Presley, auren na su ya yi ƙarƙon shekaru biyu ne kacal, daga shekara ta 1994 zuwa shekara ta 1996. 

Ta biyun kuwa ita ce Debbie Rowe, wadda ya aura daga shekara ta 1996 zuwa shekara ta 1999, zaman na su ya kwashe shekaru uku kenan. 

Ya mutu ya bar ‘ya’ya uku, babbar Paris Jackson, sai Prince Jackson da kuma Prince Michael Jackson II.

Mawaƙin wanda ake yi wa laƙabi da Sarkin gambarar zamani, Michael Joseph Jackso, ya yi rayuwa ta jin daɗi da soyayyar mutane ta ban mamaki, domin shine mawaƙi na farko da soyayyarsa ke sa wasu kuka ko suma ta sanadiyyar jin waqarsa ko ganin fuskarsa.