Ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin ɗan Adam kuma lauya, Femi Falana, tare da ɗansa Folarin, wanda aka fi sani da Falz, sun nemi Bobrisky ya janye zarge-zargen ɓatanci da ya yi musu, tare da neman gafara cikin sa’o’i 12. Wannan kira ya zo ne a ranar Laraba, bayan wani sautin murya da ke yawo a yanar gizo, inda aka ce fitaccen mai sanya kayan mata, Idris Okuneye (Bobrisky), ya yi zarge-zargen kan su.
A tuna cewa, a cikin makon da ya gabata mai sharhi na kafofin watsa labarai, Martin Otse, wanda aka fi sani da VeryDarkMan, ya fitar cewa Bobrisky ya yi ikirarin cewa ya yi magana da Falz yana roƙon taimakonsa wajen tuntuɓar mahaifinsa (Falana) domin samun afuwar shugaban ƙasa. Bobrisky ya ce ya kashe Naira miliyan 10 don wannan tsari.
Haka kuma, Bobrisky ya yi zargin cewa ya roƙi Falz ya ba shi Naira miliyan 3 don samun kulawa ta musamman a gidan gyaran hali na Kirikiri.
A cikin wani sauti daban da VeryDarkMan ya saki, Bobrisky ya ce ya biya Naira miliyan 5 ga wani Lauyan Babban Kotun Najeriya (SAN) domin neman afuwar Gwamnatin Tarayya a kan tuhumar da hukumar EFCC ta yi masa.
Sai dai, a cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 14 ga Oktoba, 2024, da lauyoyin Falana, Olorunfemi Akinyemi da Taiwo E. Olawanle suka fitar, an zargi Bobrisky da yin ƙarya da zarge-zargen ɓatanci da suka shafi Falana da ɗansa, kan batun cin hanci da neman afuwa.
Lauyoyin sun bayyana zarge-zargen Bobrisky a matsayin marasa tushe kuma waɗanda ke ɓata suna da mutuncin Falana. Sun nemi cikakken janye waɗannan zarge-zargen tare da neman gafara da za a fitar a dukkanin kafofin da aka raba wannan bayanin.
