Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Nijeriya, IPMAN, ta yi ƙarin bayanin dagane da matsayar da suka cimma da matatar mai ta Dangote kan farashin da za su ringa siyen man fetur daga wajensa.
Kungiyar ta ce, kamfanin Dangoten ya amince da sayar musu da man fetur ɗin kan Naira 990, yayin da kuma masu deport, su kuma zai riƙa sayar musu da shi kan naira 940.
Kungiyar IPMAN ta ƙulla yarjejeniya da matatar man Dangote domin ɗauke man fetur kai tsaye.
Shugaban ƙungiyar IPMAN na ƙasa, Abubakar Garima, ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai ranar Litinin a Abuja, bayan wani taron kwamitin ayyuka na ƙungiyar na ƙasa.
Ya yi bayanin cewa matatar man Dangote ta tilasta wa IPMAN ta ɗaukar man fetur, kalanzir da kuma dizal kai tsaye domin ci gaba da kawowa ma’aikatun IPMAN da kantuna.
Wannan sabon tsari da matatar man Dangote zai tabbatar da tsayuwa kuma ba a daina samar da kayayyakin man fetur a duk faɗin Nijeriya cikin farashi mai rahusa.
