Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Sabbin alƙaluman da Hukumar ƙididdigar Nijeriya ta fitar sun nuna cewa an samu raguwar hauhawar farashin kaya a watan Agusta idan aka kwatanta da watan Yulin da ya gabace shi.
NBS ta nuna cewa an samu raguwar kashi 1.76 a watan Agustan saɓanin watan Yulin.
Rahoton ya ƙara da cewa, “farashin ya tashi zuwa 126.8 a watan Agustan 2025, yana nuna ƙaruwar maki 0.9 daga 125.9 da aka rubuta a watan Yuli”.
“Halin farashi na watan Agustan 2025 ya nuna raguwar kashi 1.76 idan aka kwatanta da na Yuli na 2025.”
ƙungiyoyin birane sun fuskanci koma baya sosai, inda hauhawar farashin kayayyaki ya ragu zuwa kashi 19.75 cikin ɗari idan aka kwatanta da kashi 34.58 a cikin watan Agustan 2024. Haɓakar hauhawar farashin kayayyaki a yankunan karkara, yayin da ya ɗan yi girma, ya ragu zuwa kashi 20.28, ya ragu daga kashi 29.95 a bara.
A kowane wata, hauhawar farashin kayayyaki a birane ya ragu zuwa kashi 0.49 daga kashi 1.86 cikin ɗari a watan Yuli, yayin da yankunan karkara suka samu kashi 1.38 bisa ɗari, wanda ke nuna ci gaba da ƙalubalolin sufuri da ke ci gaba da hauhawa farashin yankunan karkara.
Farashin abinci, wanda ke da kaso mafi yawa a cikin kwandon hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya – ya kuma nuna sauƙi. Haɓakar farashin kayan abinci ya ragu zuwa kashi 21.87 cikin ɗari a duk shekara, inda ya ragu da kashi 37.52 cikin ɗari a shekara da ta wuce.
Farashin kayan abinci na wata-wata ya ragu zuwa kashi 1.65, idan aka kwatanta da kashi 3.12 a watan Yuli, sakamakon faɗuwar farashin kayan masarufi kamar shinkafa, garin masara, gero, semolina, garin masara, da madarar waken soya.
Duk da wannan matakin, NBS ta yi gargaɗin cewa farashin abinci ya ci gaba da nuna turjiya, musamman a jihohin Arewa inda rashin tsaro, rashin ababen more rayuwa, da guraben kayan aiki ke ci gaba da kawo cikas.
Babban hauhawar farashin kayayyaki – wanda ya keɓance samfuran noma da kuzari – an ƙididdige shi a kashi 20.33 cikin ɗari duk shekara, ƙasa da kashi 27.58 da aka samu a watan Agusta 2024.
Rahoton na hukumar NBS na zuwa ne kwanaki bayan da Shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya bayar da umarnin karya farashin kayan abinci ƙasar.
A watanin baya-bayan an riƙa samun raguwar hauhawar farashin kayyaki a ƙasar.
A baya dai dai an yi ta kiraye-kirayen gwamnatin ƙasar ta ɗauki matakan rage hauhawarar farashi domin magance tsadar rayuwa da ake fuskanta a ƙasar.
