Farashin kayayyaki ya ƙaru da kashi 22.22 a Nijeriya – NBS

A halin da ake ciki, farashin kayayyakin masarufi a Nijeriya ya ƙaru zuwa kashi 22.22 a watan Afrilu saɓanin 22.04 a watan Maris.

Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da Hukuma Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta fitar a ranar Litinin.

A cewar Hukumar, ƙididdigar hauhawar farashi ta watan Afrilun 2023, ta nuna an samu ƙarin kashi 0.18 na tsadar kayayyaki idan an kwatanta da watan Maris da ya gabata.

NBS ta ce bisa la’akari da sheka-shekara, an samu hauhawar farashi mai yawa a Afrilun bana idan aka kwatanta da yadda lamarin yake a Afrilun 2022, wato kashi 16.82.

Hukumar Abinci da Harkokin Noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO), ta ce a karon farko cikin shekara guda an fuskanci hauhawar farashin kayan abinci a watan Afrilu.

Hukumar ta bayyana hakan ne cikin wani rahoton da ta fitar a ranar Juma’a da ya danganci hauhawar farashin kayan abinci a kasuwannin duniya.