Mutuwa rigar kowa!

Assalam alaikum. Da farko ina roƙon Allah Ya jiƙan Jamilu Yakub (Markaz).

Mutuwa ƙarar kwana ce, domin kuwa, kowa da tanadin kwanakin da aka yi masa. Ke nan muna iya cewa, mutuwa riga ce da kowa sai ya sanya ta ko mai matsayi ko iko.

Wannan ne ya sanya mutuwa ta kasance wa’adi da kowa ke jiran nasa. Saboda haka muna iya cewa mutuwa ƙa’ida ce da kowa sai ya cika, matuƙar an hura masa rai.

Bisa irin wannan tunani ne waɗansu ke ganin mutuwa hutu ce ga kowane mamaci, musamman idan aka yi la’akari da kujuba-kujubar da mutane ke fama da su na rayuwa, kafin tafiya.

Ke nan ita kanta mutuwa balaguro ce, da dole kowa sai ya yi tattaki domin isa ga wani matsuguni. Matsuguni kuwa ga ɗan Adam dole ne, tamkar mutuwa wadda ta kasance ƙarshe ce, matabbata ce ga kowane mahaluƙi.

Duk da wannan fasalce-fasalcen mutuwa da yawan yanayenta muna iya ƙarawa da cewa mutuwa tonon silili ce, tun ba a isa ga madakata ba.

Waɗannan bayanai ina tsammanin ba sa buƙatar ƙarin haske ko kuma nanatawa, domin sun faru, suna faruwa, kuma za su ci gaba da faruwa har ranar kashe mutuwa ita kanta.

Sai dai abin da ke da muhimmanci ga kowane zan Adam shi ne ya fahimci sirrin da ke tattare da mutuwa da kuma tonon sililin da ta ke yi wa rayuwa kafin ta wuce.

Ta haka ne nake zaton za mu qara nakaltar rayuwar da muke ciki, kafin mutuwa ta yi mana sallama.

Abin da ya dace mu soma da shi a nan bai wuce ƙoƙarin fahimtar me ya sa ita rayuwa ta ke kasancewa a bisa faifai a koyaushe ba, amma kuma mu kasa fahimtar abin da ta bayyanar har sai mutuwa ta bayyanar, ta tona asirin duk wanda ta cimma a cikin zangon tafiye-tafiye na yau da kullum?

Me ya sa duk da cewa haɗarin rayuwa yana kulluwa ne a gabanmu, amma kuma sai ya zo ya iske mu ba mu shirya wa ambaliyar ruwan saman da haɗarin zai antayo da shi ba?

Mu ne da kame-kame da guje-guje da neman mafita a lokacin da komai ya jagule, ya rikirkice har sai ruwan ya yi mana dukan tsiya!

Me ya sa duk da cewa tufafin rayuwa farare su ke, amma mu ƙare da ƙazancewa a lokacin da mutuwa ta zo, mu zamanto cikin dauɗa, kayayyakin namu su yi baƙin ƙirin?

Me ya sa muke barin mutuwa na tona mana asiri, alhali muna iya rufe asiran cikin kwando ko wani abu makamancin haka?

Sai dai ina son a kula da wani abu, ni ba tonon asirin da mutuwar ke yi wa mamata ba ne ke damuna, illa irin yadda muke mance abubuwan da rayuwar ta tanada kafin a kai maƙabarta.

Abubuwan da na gani ko na ji game da wannan matsala suna da yawa, amma zan fi mayar da hankali kan biyu ko uku a wannan karon.

Na farko, tun muna ƙanana na sha nazarin yadda mutuwa ke zuwa afujajan a cikin al’ummarmu da yadda muke kallon irin ‘ɓarnar’ da ta ke yi mana, amma ba wai na tono asiri ko na silili ba.

Lallai mun san za a mutu, amma mamata ba sa kasancewa cikin takura ko matsi na yanayin da hakan ya faru gare su.

Haka kuma waɗanda aka bari a baya, su ma ba sa shiga cikin ƙunci da rayuwar ni-’yasu, domin kuwa kafin a kai ga kushewar an tanadi abubuwan da suke muhimmai dangane da rage wa mai niyya zuwa madakata, domin ya tafi cikin kwanciyar hankali da godiya, domin Allah Ya sanya yana tare da ’yan uwa da abokan arzikin da sun yi iya ƙoƙarinsu domin agazawa, amma da yake mutuwa tamkar barci ce, barauniya ce, sata take yi, dole a tafi, koda ba shirya ba, ya sa ba mai kukan tonon asiri ko damuwa da yadda gaba za ta kasance.

Shi ya sa a wancan lokaci yara qanana irinmu, har murna muke yi idan an yi kira da a matso zuwa ga makara, duk da cewa ba a bari mu kai gare ta, bare mu taɓa ko mu kama wajen ɗauka, duk da haka da zarar makara ta shiga ƙuryar masallaci bayan an dawo rakiyar masu zuwa kushewa, daɗi da annuashuwa ke biyo baya ga yara.

Abinci dai ba abin damuwa ba ne, abin sha da ma akwai a wajen makwabta da iyalan mamata. Abin da ya kasance ƙari shi ne kwabban sadaka da yara ke kwasa daga hannun mutanen unguwa domin a isar da ladar ga mamaci.

A wancan lokaci ba mai damuwa da matsaloli ko tunanin yaya za a yi da ’ya’yan da aka bari. Wa zai ɗauki ɗawainiyar karatu da ci da su da makwancinsu da sauran al’amurran yau da kullum, domin kuwa al’umma ce guda, tamkar tsintsiya.

Ke nan da wuya a ce an yi rashi. E, an yi rashi kam na ma matuƙar, domin ba za a sake ganinsu ba yadda aka saba a cikin gida ko bakin garka ko masallaci, amma iyalansu sun san ba su yi rashin abubuwan rayuwa ba, domin an tanadi abubuwan da za su agaza musu, waɗansu ma tanadin na har abada ne.

A wancan lokaci ne ake maganar agola, idan mahaifiya ta sake aure, ’ya’yan su kasance tamkar ’ya’yan sabon maigidan da suka samu kansu a ciki.

In kuma wata mutuwar ta ratsa, ɗorawa kurum za a yi, tsofaffin agola su sake komawa sababbin agola a wani gidan, su kuma sababbin agola, su samu sabon matsuguni ko a wani sabon gida ko a tsakanin kawunnai da goggonai da innoni da babanni.

Waɗansu yaran ma ba su iya tuna rashin da suka yi, in ba na zahirin rashin ganin iyayensu ba. Rayuwa tafiya take kamar ba a samu tuntuɓe ba.

Daga ƙarshen, ina mai miƙa Ta’aziyya ta ga iyalan Malam Jamilu Yakub (Markaz), Allah jaddada Rahma gare shi.

Wasiƙa daga Sayyida Alkazeem M. Shareef Alhasan, 08062740226.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *