Daga AMINA YUSUF ALI
Akwai yiwuwar farashin man fetur a Nijeriya ya yi raga-raga in dai har farashin ɗanyen man fetur a duniya ya cigaba da faɗowa.
A tarihi dai an riga an san cewa duk lokacin da farashin mai ya ɗaga a duniya, to farashin man fetur yana ƙaruwa a gidajen mai a Nijeriya ma.
Alal misali ma wannan tsadar man fetur da ake fama da ita a Nijeriya ta afku ne sanadiyyar tashin farashin ɗanyen man fetur a duniya a karo na farko a watan Mayun shekarar 2023.
Saboda haka, ake tunanin a halin yanzu da farashin ɗanyen man ya faɗi a duniya, ana sa ran tunda yanzu farashin ɗanyen mai ya sauka a duniya, ana sa ran shi ma farashinsa a gidan mai zai ragu yadda talakan Nijeriya zai saye shi da araha.
A nazarin da jaridar Nairametrics ta yi a kan farashin ɗanyen man fetur na duniya da ta yi a ranar Talata, raunin tattalin arzikin ƙasar Chana shi ya sa aka samu ɗan sassauci a kasuwar ta man fetur.
A ranar Talata dai da ma farashin ɗanyen man shi ne, Dalar Amurka $83.93 a kan kowacce ganga.
A makon da ya gabata dai ya kasance kimanin Dalar Amurka $85 a kan kowacce ganga.
Bayan kwanaki bakwai ne da wancan farashin kuma sai kasuwar ta sake faɗuwa bayan samun rahoton raunin tattalin arzikin ƙasar.
A cewar Babban Bankin Ƙasar Chana, a halin yanzu ƙasar tana fuskantar ƙalubale kala-kala a fannin tattalin arziki.
Amma Reuters sun yi hasashen cewa, akwai yiwuwar samun hauhawar farashin a ƙasar Amurka, ƙasar da ta fi ko’ina amfani da man fetur.