Gare ku Ministocin Tinubu

Ga dukkan alamu a wannan sabuwar gwamnati ta Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ta miƙa wa zaƙaƙurai wuƙa da nama ta fuskar sabbin ministoci da aka rantsas su 45 duk da dai a ranai ta Litinin ana da tabbacin ida kawo wasu cikin mutane uku su zamo 48 kamar yadda tun farko shugaba Tinubu ya aika ma majalissa jerin sunayen su.

Mu dai a yanzu saon mu su ba maraɗa kunya ai gwamnati mai faɗa da cikawa wacce za mu ce madalla da ku.

Batun tallafi na rage raɗaɗin cire tallafin mai wanda a ka fara. Babu yabo kuma ba bu fallasa domin tun a yanzu wasu sum fara ƙorafe-ƙorafe imma dai sun je ba a ba su ba ko kuma yadda a ka za ta ashe abun bai kai haka ba.

Duka dai fatammu a kula talakawa na cikin uku ba wacce sular cire tallafin mai ya janyo don haka a tausaya kuma ai adalci ganin yadda ita wannan rayuwa ba bu yanayi mai ɗorewa ga kowa.

Allah ya ba da ikon ai wannan rabo a cikin nutsuwa da adalci ga kowa. Allah ya jishe mu alkhairi.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa Katsina.07066434519 /08080140820.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *