Dandalin shawara: Na kama matata da abokina, amma na kasa sakin ta (2)

Ci gaba daga makon jiya

Tare Da AISHA ASAS

Abu na farko kamar yadda ka faɗa kana son matarka, kuma na lura sosai, zai iya yiwa tsananin son da ka ke yi mata ya wuce tunanin ka, takan yiwu kana son rabuwa da ita saboda kana cikin matsanancin fushi da ita kan cin amanar da ta yi ma ka, amma wannan fushin naka bai shafi ɓangaren da ka mallaka mata a zuciyarka ba, don haka duk fushin da ka ke yi da ita, zuciyarka ba za ta iya lamunce wa rabuwa da ita ba.

Idan kuwa hakan ne zancen, kana buƙatar fara amsar kana yi mata irin wannan so, kafin ka lalabo inda yake don samun damar rarashin shi har ya amince da hukuncin da ka yanke, wannan na nufin amincewa ka shirya shiga ƙuncin rashinta bayan ka rabu da ita.

Sai mataki na biyu, wanda na fi tunanin ka fi raja’a kansa, wato dai asiri matarka ta yi ma don kar ka iya sakin ta. Zai iya yiwa hakan domin ana yi, kuma yakan yi tasiri a wasu lokuta. Sai dai kafin yanke hukunci sai ka fara tambayar kanka wasu tambayoyi kafin ka yanke hukuncin magani ne aka yi ma. Na farkon kai kaɗai ne mai iya sanin amsar shi, yayin da ka yi yunqurin sakin matarka ya yanayin abinda ka ke ji yake?

Masana kan sha’anin da ya shafi sihiri sun ce, yayin da ka kasa aikata wani abu da ka ke so ka yi, ko kana wani abu da ka ke jin ba shi ka ke son ka yi ba, ta yadda za ka iya bambancewa shi ne; idan zuciyarka ke son ka aikata wani abu da kai ba ka so, to tana ƙoƙarin ganin ta ja ra’ayinka ne, ta hanyar rarashi da ƙawata maka shi, har sai ka wayi gari ka biye mata, wanda Bahaushe ke kira son zuciya, ma’ana kana biyayya ga abinda zuciyarka ke so. Kenan za ka yi ne cikin amicewarka.

Idan sihiri ne kuwa zai kasance abu na tursasawa domin zuciyarka ma zata yi ba tare da so ba. Misalin ababen biyu shi ne, iyayenka su ce sai ka yi abinda kai ba ka yi niyyar yi ba, da kuma matarka ta so ka yi mata abinda ta san ba ka so ka yi.

Iyayenka za su sanar da kai abinda suke so ka yi, kuma ko ba ka so za ka yi cikin tursasawa, amma dai za ka yi. Ita kuma matarka ga mai hankali zata kwantar da kai, cikin kissa da rarashi har ta shawo kansa ya yi abin cikin jin daɗi ko amincewa.

Alama ta biyu, a yayin da ka yi haramar bijerewa abinda sihiri ke saka aikatawa, za ka haɗu da ɗaya daga cikin biyu, ko dai matsanancin ciwon kai da zai gigitaka ka fasa ƙudurinka cikin gagawa, ko kuma fita hayyacinka har sai ka canza ra’ayi.

Za mu kai ƙarahe a sati mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *