Shugabannin Nijeriya ku ji tsoron Allah

Tun lokacin da shugaba Tinubu ya ayyana janye tallafin fetur tun kafin lokacin da Shugaba Buhari ya ayyana zai janye, Amma ya dakatar zuwa watan Juni saboda ’yan takardar APC sun buƙaci a dakatar don su ci zaɓe.

Kuma an dakatar sun yi kamfen buƙatar su ta biya, madadin ya tsaya ya nazarci ƙasar da matsalolin ta bai yi hakan ba nan take ya aiwatar kuma aikin gaggawa da na sani ke biyo baya.

Hankalin ’yan siyasa ya kwanta mutane sun afka cikin yunwa da talauci da rashin aikin yi mutane basa iya zuwa aiki masu abin hawa sun ajiye, asibitoci sun cika da majinyata.

Kai har makabartu yawan gawarwaki da ake Kaiwa ya fi na baya buƙatar su ta biya an shiga mawuyacin hali hatta dabbobi sun shaida wannan masifa.

Babu abin da ya rage wa talaka illa ya ci gaba da addu’a dukkan masu assasa wannan manufa ta janye tallafin mai da wanda suka aiwatar da masu amfana da masu jin daɗi Allah ya shiga lamarin ya ceci bayinsa ya mana maganin su ruwan sanyi.

Allah ya sa kada mu gaza Allah ya ba kowa mafita tun kafin wahala ta iske wanda bai zaci za ta iske shi ba.

Daga MUAZU HARDAWA Edita Jaridar Alheri Bauchi Dandalkura radio reporter. 08062333065.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *