Talakawa sun wawushe rumbun ajiyar kayan abincin gwamnati a Bayelsa

Daga BASHIR ISAH

A ranar Lahadin da ta gabata talakawa a Jihar Bayelsa suka yi wa rumbun ajiyar gawamnatin jihar da ke yankin Kpansia a Yenagoa babban birnin jihar dirar mikiya tare da wawushe kayan abincin da ke adane a cikinsa.

Majiyarmu ta ce kayan abincin da jama’a suka kwashe sun haɗa da buhunan shinkafa da garin kwaki da sauransu.

Tuni dai gwamnatin jihar ta bakin Hukumar Bada Agajin Gaggawar Jihar (BYSEMA) ta yi tir da wannan aika-aikar.

Cikin sanarwar da ta fitar, hukumar ta ce ma’ajiyar mai zaman kanta ce, tana mai cewa lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 7:45 na daren Lahadi, 27 ga Agusta, sa’a guda bayan da Darakta-Janar na hukumar, Walamam Igrubia tare da tawagarsa suka bar ma’ajiyar.

A cewar hukumar, an yi amfani da rumbun ne wajen adana kayan abinci yayin ambaliyar ruwan da aka fuskanta a 2022.

“A matsayin shirye-shirye domin daƙile matsalar ambaliyar ya sa Darakya-Janar ya ziyarci rumbun inda sauran kayan abincin ke adane da suka haɗa da shinkafa garin kwaki, kuma kayan abinci sun lalace,” in ji sanarwar.

Hukumar ta ce kayan da ke adane a rumbun sun lalace ta yadda babu yadda za a yi gwamnati mai hankali ta raba wa jama’arta a matsayin tallafin rage raɗaɗi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *