Fasfon Yahaya Bello yana hannun Babbar Kotun Tarayya, ba wurinmu ba, inji Babbar Kotun Abuja

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Babbar Kotun Birnin Tarayya, Abuja ta bayyana a ranar Alhamis cewa fasfo ɗin tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ba ya hannunta, amma yana hannun babbar kotun tarayya da ke Abuja.

A zaman da aka ci gaba da sauraron aarar da Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin ƙasa Zagon ƙasa (EFCC) ta kafa a kan tsohon gwamnan, Mai Shari’a Maryann Anenih ta ce kotu za ta duba buƙatar sakin takardar tafiye-tafiyen wanda ake ƙara idan har tana hannun ta.

Ta ce, ko da an amince da buƙatar sakin fasfo ɗin, hakan ba zai yi wani tasiri ba tunda fasfo ɗin ba a hannun babbar kotun Abuja, sai dai a hannun kotun tarayya da ke babban birnin tarayya Abuja, a gaban Mai Shari’a Emeka Nwite.

Tsohon gwamnan dai yana fuskantar irin wannan tuhuma a manyan kotunan babban birnin tarayya Abuja da babban kotun tarayya ta Abuja.

Ya gabatar da takardar neman a ba shi fasfo ɗinsa domin samun damar fita daga aasar bisa dalilan lafiya.

A baya lauyan wanda ake ƙara Joseph Daudu, SAN, ya gabatar da cewa fasfo ɗin da ake nema ba ya hannun kotu.

Binciken bayanan kotun ya nuna cewa a baya an umarci Yahaya Bello ya ajiye fasfo ɗinsa da sauran takardun balaguro zuwa wurin rajistar kotun.

Sai dai kuma bayan binciken kotun ta yi, an gano cewa fasfo ɗin ba ya hannun bangaren rajistar kotun, a yanzu haka yana hannun babbar kotun tarayya ne.

Shi ma wanda ake tuhuma a cikin buƙatarsa, ya kuma nuna cewa takardun tafiyarsa na tare da babbar kotun tarayya.

Mai Shari’a Anenih, bayan yanke hukuncin, ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 8, 9 ga watan Oktoba; da Nuwamba 13, 2025.

A ranar 8 ga watan Yuli ne kotun ta ɗage yanke hukunci kan buƙatar wanda ake wara zuwa ranar Alhamis 17 ga watan Yuli.

Daudu, SAN, ya shaida wa kotu cewa an shigar da ƙarar ne ranar 19 ga watan Yuni, 2025.

By ukarofi