
Daga BELLO A. BABAJI
A yammacin ranar Alhamis ne wata tankar man fetur ta tarwatse a ƙauyen Ƙaramin Rami na ƙaramar hukumar Mashegu a jihar Neja, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane bakwai.
A wata takarda da Darakta-Janar na Hukumar bada Agajin Gaggawa ta jihar, Abdullahi Baba Arah ya fitar, ya ce lamarin ya auku ne a lokacin da tankar ta yi ƙoƙarin canza hannu sakamakon rashin kyan hanya, inda ta faɗi tare da kwararar da man da ke cikin ta a wani wajen da manoman rani na shinkafa ke aiki.
Ya ce, man da ke zubar ya haɗe ne da famfon ban-ruwa da manoman suke amfani da shi, wanda hakan ya yi sanadin kamawar wuta tare da tarwatsa tankar.
Ya bayyana cewa, wutar ta yaɗu ne a gonakin manoman inda akwai wani gurɓataccen ruwa, wanda ya sabbaba ƙonewar wasu daga cikin manoman da lalata baki ɗaya filin aikin shinkafar da wani yanki na ababen marmari.
Lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane bakwai da raunata guda ɗaya.
Waɗanda suka rasa rayukansu sun haɗa da Rafi’atu Sahabi, Ramlat Shehu, Rashida Abdullahi, Raliya Abdulrahman, Zainab Ahmed, Zuwaira Idrisu da Maryam A. Nura, sai kuma Maimuna Isah, wadda aka kai ta Asibitin Saho Rami Primary Health Care sakamakon raunukan da ta samu.