
Daga BELLO A. BABAJI
Babbar Jam’iyyar adawa, wato PDP, ta yi alla-wadai da dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan daga Majalisar Dattawa sakamakon zargin cin zarafi da ta yi akan Shugaban majalisar, Godswill Akpabio.
A ranar Alhamis ne majalisar ta sanar da dakatar da Sanata Natasha na tsawon watanni shida bayan samun ta da laifin taka wasu daga cikin dokokinta.
Hakan ya biyo bayan rikicinta ne da Akpabio, wanda ta zarga da yunƙurin cin zarafin ta duk da cewa daga bisani ya musanta batun.
A sanarwar da Sakataren yaɗa labaran PDP na ƙasa, Debo Ologunagba ya fitar a ranar Juma’a, jami’yyar ta ce matakin da shugabancin majalisar ƙarƙashin jagorancin Akpabio ya ɗauka akan Natasha, wata hanya ce ta yin rufa-rufa.
PDP ta ce, dakatar da Natasha ba tare da yin bincike game da zargin da ta yi ba ya nuna cewa majalisar waje ne da ke amince wa rashin daidai.
Ta kuma ce, hakan ya nuna cewa mutanen Jihar Kogi ta Tsakiya ba su da ƴancin samun wakilci a majalisar kamar yadda dokar ƙasa ta bayar.
PDP ta ƙara da cewa, idan ba ƙoƙarin rufa-rufa ake yi ba, ai da sai ya miƙa wuya ga yin buɗaɗɗen bincike akan zargin da ta yi masa don ya wanke kansa.
Har’ilayau, jami’yyar ta ce tun da Akpabio ya karɓi shugabanci, majalisar ta rasa alƙibla da samun batutuwa na haɗakar kuɗaɗe da sauransu, ta na mai bada misali da binciken da EFCC ta ke yi akan zargin sace biliyan N108.1 na gwamnatin Akwa-Ibom a ƙarƙashin jagorancin Akpabio.