Daga MUHAMMADU MUJITTABA MUJITABA a Kano
Shugaban Hukumar Ilimin Kimiyya da Fasaha ta Jiihar Kano, Farfesa ɗahiru Sale ya bayyana cewa maganar da Mataimakin Gwamnan Kano Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo ya yi a taron ‘Ranar Kimiyya da Fasaha ta Duniya’ da aka gabatar a gidan gwamnatin Kano a ranar Litinin da ta gabata, a jawabin Mataimakin Gwamna, ya bayyana cewa gwamnatin Kano ta kafa kwamitin bincike da fassara litattafan kimiyya da fasaha, “wanda abin murna ne kuma abin farin ciki ne kuma muna goyan bayan wannan abin ɗari bisa ɗari kuma zai kyakyawar fahimta cikin sauƙi musamman ga ɗalibanmu da ke makarantun kimiyya da fasaha na jihar Kano da ke ƙarƙashin wannan hukuma ta KSTSB wato Kano Science And Technical Schools Board, don haka abin a yabawa gwamnatin Kano ƙarƙashin shugabancin Alhaji Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo ne.”
Haka kuma Farfesa ɗahiru Sale ya bayyana gwamnan Kano a matsayin garkuwar ilimin kimiyya da fasaha da ma sauran fanonin ilimi musamman yadda duk kasafin kuɗinsa ilimi ya ke bai wa muhimmanci inda ya ware kashi 31 a kasafin wannan shekara na 2025 mai zuwa da yardar Allah kuma irin wannan gudunmawar ta gwamnan Kano ce ta sa yanzu haka a taron da aka yi na makon kimiyya da fasaha da ranar kimiyya da fasaha ta duniya da ma’aikatar bunƙasa ilimin kimiyya da fasaha ta yi ƙarƙashin Hon. kwamishina Mohammed Tajo Othman ta shirya tare da bajekolin fasahar ɗalibai da sauran matasa da kuma shirya gasar wasa ƙwaƙwalwa da kacici kacici da ma’,aikatar ta shiryawa ɗaliban makarantu kimiya da fasaha na jihar Kano a tsakanin makarantun gwamnati da masu zaman kansu, inda makarantun kimiyya da fasaha na gwamnatin Kano suka zama kan gaba wajen samun kofi da kyaututuka a wannan rana.
Ya ce hakan ya nuna cewa makarantun kimiyya da fasaha na gwamnatin Kano ba kanwar lasa ba ne, inda ya ce hakan ta faru ne kan kulawar gwamnan Kano a fannin ilimi.
A ƙarshe ya ce irin tsare tsare da cibiyoyi koyar da kwamfiyuta domin jarrbawa da sauran ilimi ga ɗalibai shima abin a yabawa gwamna ne musamman ganin yadda wannan hukuma ta ke samun haɗin kai daga gwamnan Kano ko da yaushe.
