GKM ta horar da marayu 30 sana’o’in dogaro da kai 

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano 

Shugabar gamayyar ƙungiyoyin mata marayu da masu buƙata ta musamman ‘GKM Organization’ ƙarƙashin shugabancin Hajiya Balaraba Goga ta bayyana cewa wannan ƙungiya ta horar da marayu matasa mata sama da 30 sana’o’in dogaro da kai a wannan lokaci kamar yadda ta bayyana a wajen bikin ƙaddamar da littafin da wannan ƙungiya ta rubuta domin faɗakar da al’ummar Arewa da ma Nijeriya baki ɗaya.

Taron dai ya gudana ne a gidan tunawa da Marigayi Malam Aminu Kano da ke Unguwar Gwammaja a ƙarshen makon nan.

Taron da ya samu halartar masu rajin tallafawa marayu da raunana ya samu halartar Jarman ƙasar Sarkin Dillalan Kano, Alhaji Ado Abdullahi Sharaɗa, inda ya yaba wa shugabar ƙungiyar GKM da sauran waɗanda suke tallafa mata da sauran marayu inda ya buƙaci al’umma da ta yi koyi da wannnan baiwar Allah wajen agazawa marayu da raunana ta hanyar da koyar da sana’o’i da kuma tallafa musu ta fannin ilimi 

Shi ma shugaban tashar manyan motocin sufuri da ke bypass Kano Alhaji Kabiru Kureken Sani Mai Unguwa ya bayyana farin ciki da kuma jawo hankalin gwamnati da mawadata da sauran al’umma muhimmanci da kuma wajibcin taimakawa marayu da raunana da abin da Allah ya hore masa komai ƙanƙantarsa.

A ƙarshe Hajiya Balaraba Goga ta yaba wa ɗaukacin waɗanda suka halarci wannan taro da kuma bada gudunwarsu ta hanyar ƙaddamar da littafin da aka rubuta don neman agaji da cigaba da tallafawa marayu da raunana da masu buƙata ta musamman.

An dai tara maƙuɗan kuɗaɗe a ƙaddamar da wannan littafin don cigaba da taimakawa marayu da masu buƙata ta musamman a wannan lokaci da rayuwa ta ke da matuƙar buƙatar taimakawa marayu da raunana.

By ukarofi