Falana ya soki Wike kan rabon gidaje ga alƙalai a Abuja 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Femi Falana, lauyan kare haƙƙin ɗan’adam, ya soki Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya (FCT), kan bai wa alƙalai gidaje.

A watan Satumba, ministan ya ƙaddamar da gina gidaje 40 don alƙalai a Abuja, wanda ya tayar da hankula a cikin al’umma.

Ya ce daga cikin gidajen, 20 za a ware su ga alƙalai na babbar kotun FCT, 10 kuma za a bai wa alƙalai na babbar kotun tarayya, sannan 10 kuma ga alƙalai na kotun ɗaukaka ƙara.

Manhaja ta rawaito cewa duk da haka, a ranar Laraba, Wike ya musanta zargin cewa gidajen ana ginawa ne don ya mallaki alƙalai domin samun fa’ida ta siyasa.

Ya ce gina gidajen don alƙalai wani ɓangare ne na shirye-shiryen walwala da Shugaba Bola Tinubu ya tsara don inganta ‘yancin ɓangaren shari’a.

A yayin da ya ke martani kan lamarin a wata hira da aka yi da shi a Politics Today, wani shirin talabijin na Channels, a ranar Laraba, Falana ya ce alƙalai ba su da dalilin zuwa ga ɓangaren zartarwa don a saya musu motoci da gidaje.

Babban lauyan mai matsayin SAN ya ce cin gashin kai na ɓangaren shari’a ya kasance cikin kundin tsarin mulki.

Ya ƙara da cewa hukumar kula da fannin Shari’a ta ƙasa, NJC, ce ta kamata ta ɗauki nauyin raba gidaje ga alƙalai ba ministan Abuja ba.

By ukarofi