TCN ta nuna damuwar ta kan sace-sacen wayoyin lantarki a Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Nijeriya (TCN) ya bayyana matuƙar damuwarsa kan yadda ake samun ƙaruwar matsalar sace-sacen wayoyin lantarki, inda ta yi gargaɗin cewa wannan lamari yana matuƙar kawo cikas ga hanyoyin samar da wutar lantarki da ababen more rayuwa a ƙasar.

Babbar Manajan Hulɗa da Jama’a na TCN, Misis Ndidi Mbah, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar yayin da take mayar da martani game da lalata layin sadarwa mai ƙarfin kɓ 330 daga Lokoja-Gwagwalada I.

“A halin yanzu, TCN ta ruwaito cewa barayi sun sake kai hari kan layinta mai karfin 330kɓ Lokoja-Gwagwalada a safiyar ranar Asabar.

“Da sanyin safiyar ranar Asabar ne injiniyoyin TCN suka yi yunƙurin sake farfaɗo da layin ɗaya daga Lokoja-Gwagwalada mai ƙarfin 330kɓ, amma layin ya ci tura.

“Bayan ƙoƙarin dawo da layin ya ci tura, sai aka aike da tawagar ‘yan sintiri na layukan TCN domin gano kura-kuran da aka afka a layin.

“Bayan bincike, sun gano cewa an lalata hasumiya ta T306, T307, da T308 da ke kan layin ɗaya, lamarin da ya kawo cikas ga samar da wutar lantarki a kan hanyar.”

Kamfanin ya ƙara da cewa, an yi awon gaba da manyan wayoyi guda biyu daga layin, inda ake ƙoƙarin maye gurbinsu.

A ci gaba da bincike, TCN ta ce, an gano cewa ɓarayin sun saci manyan wayoyi guda biyu daga layin ɗaya.

Layin Lokoja-Gwagwalada, ya ƙara da cewa, layin sadarwa ne mai kewayawa biyu, kuma yayin da TCN ke ci gaba da samar da wutar lantarki mai yawa ta layin biyu, ana ci gaba da ƙoƙarin samar da masu maye gurbin na’urar aluminium domin tazarar biyu da aka sace daga layin ɗaya.

By ukarofi