Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Kare Masu Saya da Amfani da Kayayyaki ta Nijeriya (FCCPC) ta bayar da wani kakkausan gargaɗi ga masu bada rance ba bisa ƙa’ida ba ta intanet, waɗanda ake kira da ‘Loan Sharks’ kan barazana da tsangwamar masu karɓar rancen su, inda ta buƙaci ‘yan Nijeriya da su tashi tsaye wajen ƙwato haƙƙinsu.
A cikin wata sanarwa ranar Lahadi, hukumar ta ayyana cewa, “Bai kamata abokin ciniki ya rayu cikin tsoro ba.”
Hukumar ta FCCPC ta ƙarfafa wa waɗanda masu bada rancen ke yi wa barazana, ɓata musu suna, da kuma tozarta su da su kai ƙarar irin waɗannan ayyuka ga hukumar nan da nan.
Hukumar ta sake jaddada ƙudirinta na kare ‘yan ƙasar daga ayyukan da ba su dace ba, inda ta ce duk da cewa dole ne a biya basussukan da ake karɓa, amma bai kamata masu karɓar bashi su fuskanci cin zarafi ko tsangwama ba a cikin wannan tsari.
An yi kira ga ‘yan Nujeriya da su yi amfani da hanyoyin ƙorafe-ƙorafe na hukumar ta FCCPC domin fallasa masu cin zarafin su kan rance yayin da hukumar ke ƙara zage damtse kan ‘yan damfara a fannin hada-hadar kuɗi.
