
Daga BELLO A. BABAJI
Hukumar Raya Birnin Tarayya (FCTA), ƙarƙashin umarnin Ministan Abuja, Nyesom Wike ta ce daga ranar Litinin za ta karɓe iko da filaye guda 4,794 bisa rashin biyan kuɗaɗen hayar ƙasa na shekaru tsakanin 10 da 43.
Daga cikinsu akwai na Sakatariyar jam’iyyar PDP dake birnin, wanda an ƙwace shi tun a watan Maris na wannan shekarar saboda rashin biyan kuɗin haya na shekaru da dama.
Mai taimaka wa ministan kan harkokin yaɗa labarai, Lere Olayinka ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai, ranar Juma’a.
Ya ce, tuni FCTA ta ƙwace mallakar filayen, waɗanda ke yankunan Central Area, Garki na 1 da na 2, Wuse na 1 da na 2, Asokoro, Maitama da kuma Guzape.
Ya kuma ce, za a yi hakan ne bisa aiki da doka da tsarin gudanarwar hukumar ba tare da la’akari da na waye ne ko wa hakan ya shafa ba.
Daraktan kula da harkokin ci-gaban birni, Mukhtar Galadima ya ce za a rufe wuraren da abin ya shafa tare da sanya alamar hana shiga ko amfani daga ranar Litinin.
Ya bayyana cewa, FCTA za ta yanke abinda za ta yi da filayen a dokance.
Game da waɗanda suka shigar da ƙara a kotu, daraktan ya ce babu wani hukuncin kotu akan ƙwace filayen, yana mai cewa hukumar ta yi abinda ta ke da iko a kai ne.
