Fethullah: Babu ɓullar sabuwar ƙungiyar ta’addanci a Nijeriya – Hedikwatar Tsaro

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta musanta iƙirarin da jakadan Turkiyya a Nijeriya, Mehmet Poroy ya yi na cewa wata ƙungiyar ta’addanci na gudanar da ayyukan ta a cikin yankunan Nijeriya a ƙarƙashin tsarin ilimi da kiwon lafiya.

A wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na tsaro, Manjo Janar Markus Kangye ya fitar a ranar Alhamis, hedikwatar ta bayyana wannan iƙirari a matsayin “maganar ba a hukumance ba” kuma ba ta da tushe mai inganci, tana mai cewa Nujeriya a matsayinta na ƙasa mai cin gashin kanta, ba ta yarda da bayanan sirri na ƙasashen waje ba tare da tantancewar ta ba.

“Hedkwatar tsaro ba ta yarda iƙirarin jakadan Turkiyya ba. kowa yana da ‘yancin faɗin duk abin da yake so. Akwai ‘yancin samun bayanai,” inji Kangye.

“Nijeriya ƙasa ce mai cin gashin kanta wacce za ta iya yin tunani da aiki da kanta.”

Ambasada Poroy da yake magana a wani taron da aka gudanar a Abuja ranar Talata da ta gabata na tunawa da ranar dimokuraɗiyya da hazin kan ƙasa ta Turkiyya, jakadan Poroy ya yi iƙirarin cewa mambobin ƙungiyar ta’adda ta Fethullah (FETO) na da ƙarfi a Nijeriya, musamman a fannonin ilimi da kiwon lafiya.

Poroy ya yi gargaɗin “Kasancewar irin wannan ƙungiya baraza ce ga kowace ƙasa da take gudanar da ayyukanta.”

Turkiyya dai na ɗaukar ‘yan ta’addar FETO a matsayin ƙungiyar ‘yan ta’adda, inda ta ɗora mata alhakin juyin mulkin da bai yi nasara ba a ranar 15 ga watan Yulin 2016 kan shugaba Recep Tayyip Erdogan.

Ana zargin ƙungiyar da alaƙa da marigayi malamin ƙasar Turkiyya Fethullah Gulen, wanda ya gudanar da harkokin makarantu da ƙungiyoyin agaji na duniya kafin rasuwarsa a shekarar 2024.

Yayin da Turkiyya ke ci gaba da muraushe cibiyoyi da ke da alaƙa da Gulen a duniya, ƙasashe da dama ciki har da Nijeriya ba su sanya ƙungiyar ta FETO a matsayin ƙungiyar ta’addanci ba, haka kuma ba su gabatar da hujjoji da ke tabbatar da irin wannan iƙirarin a Nijeriya ba.

Manjo Janar Kangye ya jaddada cewa manufofin Nijeriya na yaƙi da ta’addanci su na bin diddigin bayanan sirri na ƙasa ne, ba labaran duniya ba.

“Ba za mu iya ɗaukar abin da wasu mutane ke cewa game da Nijeriya ba, mu amince da shi ba tare da tantance ‘yancin kanmu ba, Nijeriya ta san abin da yake, kuma sojojin Nijeriya na da nata ƙa’idojin aiki da tsarin aiki.”

Ya amince da kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Nijeriya da soja da ƙasashe da dama, ciki har da Turkiye, amma ya yi gargaɗin a guji amfani da irin wadannan manhajoji wajen tallata bayanan da ba a tantance ba da za su iya tada firgici ko rashin yarda da su.

Kangye ya ci gaba da yin ishara da ƙaruwar farfagandar ƙasa da ƙasa da ayyukan tunani, yana mai gargaɗin cewa ikirari na ƙasashen waje na iya zama wani lokaci na manyan hanyoyin tafiyar da siyasar ƙasa.

“Akwai masu yaɗa farfaganda a duk faɗin duniya, shi ya sa dole ne mu yi taka tsantsan,” inji shi.

A ƙarshe ya ƙara jaddada aniyar Nijeriya na yaai da ta’addanci a ƙashin kanta, tare da jagorancin abubuwan da suka sa a gaba, da ingantattun bayanan sirri, da kuma ƙa’idojin soja da ake da su.

By ukarofi