Fetur: ’Yan ƙwadago sun buƙaci gwamnati ta sake duba mafi ƙarancin albashi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar ƙwadago ta Nijeriya, NLC, ta buƙaci a sake duba tsarin mafi ƙarancin albashin ma’aikata biyo bayan ƙarin farashin man fetur da Kamfanin Man Fetur na Nijeriya ya yi.

Shugaban ƙungiyar ta NLC, Joe Ajaero, ya yi wannan kiran a wajen taron wakilan ma’aikatan jinya da ungozoma na ƙasa karo na takwas a Abuja, ranar Laraba.

Ajaero ya ce, “A yau, ƙididdigar tattalin arzikin ƙasa gana gangarewa inda babu abin da ke tare shi. Farashin man fetur ya yi matsanancin tsada wanda ba zai yiwu talakan Nijeriya ya iya saya ba.

“Tsarin sufuri ya taɓarɓare, wanda ya haifar da ƙarancin abinci da yunwar da ba a taɓa ganin irinta ba a ƙasar nan. Muna neman a sake duba albashin mu kafin mu kasa rayuwa.”

Ajaero ya jaddada buƙatar haɗin kai a tsakanin ma’aikata, yana mai cewa, “Muna buƙatar haɗin kan ku da ƙarfin ku idan har muna son tafiyar da abubuwa yadda ya kamata.”

Ya buƙaci ƙungiyar ƙwadagon da ta ƙalubalanci gwamnati wajen neman sassaucin da kare muradun zamantakewar al’umma.

By ukarofi