Fidelity Bank ya maido da zarafin tura kuɗi zuwa bankunan OPay, Kuda, Moniepoint da Palmpay

Daga BASHIR ISAH

Bankin Fidelity ya maido da zarafin yin tiransifa ta yadda a yanzu kostomominsa za su iya ci caba da tura kuɗi zuwa bankuna irin su OPay da Moniepoint da Palmpay da kuma Kuda.

Wannan na zuwa bayan da a ‘yan makonnin da suka gabata Bankin Fidelity ya daƙile damar yin tiransifa zuwa wasu bankuna saboda yawaitar harkokin ‘yan damfara da kuma tantance kostomominsa.

Majiya daga bankin ta ce yanzu bankin ya buɗe hanyar ci gaba da tiransifa ta yadda a abokan mu’amalarsa za su ci gaba da tura kuɗi zuwa bankunan da a baya ya katse zarafin haka.

Majiya daga ɗaya daga cikin bankunan da lamarin ya shafa ta ce, “Muna tattauna da Bankin Fidelity, don haka muna sane da shirin da ya yi na maido da hada-hada a tsakaninmu.”

Bayanai sun ce Bakin Fidelity ya ɗauki matakin maido wa kostomomi zarafin ci gaba da tura kuɗi zuwa bankunan da lamari ya shafa ne biyo bayan matsin lambar da ya fuskanta daga cibiyar kula da mu’amala tsakanin bankuna, NIBSS.