Matsalar matsananciyar yunwa a Nijeriya

An yi hasashen cewa ‘yan Nijeriya miliyan 25 na iya fuskantar matsananciyar yunwa tsakanin watan Yuni zuwa Agusta 2023 (lokacin bazara) idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba don magance matsalar. Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya nakalto Cadre Harmonise a watan Oktoba na shekarar 2022, wani bincike na abinci mai gina jiki ƙarƙashin jagorancin gwamnati da Majalisar Ɗinkin Duniya, yana mai nuni da cewa an yi hasashen cewa alƙaluman na ƙaruwa daga sama da mutane miliyan 17 da ke fuskantar barazanar ƙarancin abinci a halin yanzu a Ƙasar. A cikin wannan adadi, mutane miliyan uku suna jihohin Adamawa, Borno da Yobe. An kiyasta adadin a waɗannan jihohi uku zai haura miliyan 4.4 a lokacin rani idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba.

Rahoton ya bayyana yankin Arewa maso yammacin Nijeriya musamman Katsina da Zamfara da Sakkwato a matsayin inda ake fama da matsalar ƙarancin abinci da rashin abinci mai gina jiki. A halin yanzu, an ce kimanin mutane miliyan 2.9 ne ke fama da matsalar ƙarancin abinci a yankin, kuma ba tare da ɗaukar matakin gaggawa ba, ana hasashen adadin zai ƙaru zuwa miliyan 4.3 a lokacin rani. Ya gano cewa bala’o’in da ake cigaba faruwa kamar; sauyin yanayi, hauhawar farashin kayayyaki da hauhawar farashin kayan abinci a matsayin wasu daga cikin abubuwan da ke haifar da wannan matsalar.

Jami’in kula da ayyukan jin ƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya, Mathias Schmale, ya ce, “Halin da ake fama da shi na samar da abinci mai gina jiki a duk faɗin Nijeriya na da matuqar damuwa. Na ziyarci cibiyoyin tabbatar da abinci mai gina jiki cike da yara, waɗanda ke fafutukar cigaba da rayuwa. Dole ne mu yi aiki a yanzu don tabbatar da cewa sun sami tallafin ceton da suke buƙata.”

A shekarar da ta gabata ne Hukumar Abinci da Aikin Noma ta FAO tare da haɗin gwiwar hukumar samar da abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya WFP a wani rahoto na haɗin gwiwa, ta bayyana cewa matsalar ƙarancin abinci ta ƙara tsananta a Nijeriya da wasu ƙasashe 18. Nijeriya kuma tana cikin jerin ƙasashe 10 da ke fama da yunwa a duniya, amma a lamarin ya fi ƙamari.

Ana iya gano matsalar ga rashin kula da noma. A halin yanzu, irin aikin noma da muke yi ba zai iya ciyar da ɗimbin al’ummarmu ba. Yawancin manomanmu har yanzu ba su yin noman rani. Har yanzu suna amfani da tsoffin kayan aikin noma. Sannnan wasu daga cikin manoma da muke da su yanzu suna tsoron zuwa gonakinsu. Tushen matsalar shine rashin tsaro. Jihohi uku da aka ambata a cikin rahoton sun fi muni a Arewa inda rashin tsaro ya ƙamari. Misali a jihar Borno kusan manoma 67 ne aka kashe a lokacin da ’yan ta’addar Boko Haram suka mamaye gonakinsu da ke ƙauyen Zabarmari da ke Ƙaramar Hukumar Jere a shekarar 2020. A wasu yankunan Arewa ta Tsakiya kamar Binuwai da Filato, irin wannan matsala ta faru. Waɗannan manoma dai sun sha faɗa da makiyaya da ’yan bindiga a lokuta daban-daban inda aka kashe wasu daga cikinsu. Wasu kamar jihar Zamfara, ’yan fashin faji da ’yan ta’adda na tilastawa mutane biyan haraji domin su samu ‘yancinsu. Yaƙin Rasha da Yukren da ke cigaba da yi shi ma wani lamari ne da ya taimaka wajen rashin abinci a ƙasar. Yukren dai ita ce babbar mai fitar da alkama a duniya.

Baya ga haka, an samu ambaliyar ruwa a kusan jihohi 34 na tarayyar ƙasar a bara. Ambaliyar ta kasance mafi muni a Nijeriya cikin sama da shekaru goma. Wannan ya haifar da ɓarna mai yawa ga gidaje, makarantu, shaguna da dubunnan filaye da gonaki, kuma ya haifar da qarancin abinci a ƙasar. Ya kuma shafi dabbobi da kayan abinci kamar shinkafa, dawa, da rogo. Ambaliyar ruwan ta shafi gonar noman shinkafa ta Olam da ke jihar Nasarawa da aka ce ita ce gonar shinkafa mafi girma a Nijeriya. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ana sa ran ambaliyar za ta yi sanadiyar mutuwar mutanen da ke fama da ƙarancin abinci a ƙasar.

Akwai buƙatar gwamnati ta yi wani abu game da wannan yunwa da ake hasashe. Matakin farko shi ne magance matsalar rashin tsaro a qasar. Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sha yin alƙawarin magance matsalar, amma har yanzu ba magance wannan dodo ba. Yakamata jami’an tsaronmu su kasance da isassun kayan aiki da zimma don fuskantar masu aikata laifuka a cikin al’ummarmu.

Ya kamata gwamnati kuma ta samar da yanayin da zai sa kamfanoni su ci gaba. Ya kamata kuma ta ba da kwarin gwiwa ga manoma. Muna da isasshen fili don noman abinci idan har za a iya tabbatar da isasshen tsaro, kuma gwamnati ce kawai za ta iya tabbatar da hakan.

A nasu ɓangaren, manoma na buƙatar su rungumi noman zamani. Akwai fasahohin zamani kamar fasahar ƙere-ƙere da za su iya tura su don samar da ingantacciyar amfanin gona mai yawan gaske da kuma na fitar da su zuwa ƙasashen waje. Ya kamata a ƙarfafa iri na noma waɗanda za su inganta amfanin gona. Wannan yana buƙatar sanya isassun madatsun ruwa da ƙarfafa haɗin gwiwar kamfanoni masu zaman kansu.

Manyan ƙungiyoyi, hukumomin bayar da tallafi ko kamfanoni na iya taimakawa wajen rage yunwa a ƙasar. Za su iya taimakawa ta hanyar samar wa matasanmu da ke tururuwar neman aikin yi domin babban abin da ke haddasa rashin tsaro a ƙasar nan shi ne rashin aikin yi. Wani kiyasi na masu hasashe ya nuna cewa yawan marasa aikin yi a Nijeriya ya haura kashi 33 cikin ɗari. Kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana, ana buƙatar tallafi ga iyalai masu rauni a faɗin Nijeriya a yau ba gobe ba.