Mun samu ƙorafe-ƙorafe masu yawa a Kano kan take haƙƙin ɗan Adam – Shehu Abullahi

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Hukumar Kare Haƙƙin ɗan Adam ta Ƙasa reshen Jihar Kano ta samu ƙorafe-ƙorafe da yawa a ɓangarori daban-daban na take haƙƙin ɗan Adam.

Shugaban hukumar Alhaji Shehu Abullahi ne ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida, ya ce ƙorafin ya fi shafar mata da ƙananan yara domin kuwa a wannan shekarar daga watan uku zuwa watan Oktoba sun samu ƙorafe-ƙorafe guda 1’147.

Ya qara da cewa daga cikin wannan adadi ofishinsa ya yi ƙoƙarin kammala ayyuka akan guda 1,320 sannan akwai guda 227 suna cigaba da yin ayyuka a kansu.

Shugaban na hukumar kare haƙƙin ɗan adam na ƙasa reshen Jihar Kano ya ƙara da nuni da cewa akwai wasu ɓangarori da hukumar ke gudanar da aiki akai da ya shafi ɓangaren mata da abinda ya shafi al’amuransu wanda shi ne ya ɗauki kaso mafi yawa da ƙorafi guda 907 .

Ya ce wannan ɓangare akwai ƙorafi da ya shafi rashin ɗaukar ɗawainiyar iyali suna da ƙorafi guda 720 akai da kuma ɓangaren da ya shafi rigingimu na cikin gida tsakanin ma’aurata da ya kai 150. Sannan a ɓangaren haƙƙi na yara sun samu ƙorafi 310 wanda kusan 300 ya shafi cigaban yara ne da walwalarsu sai 10 da ya shafi cin zarafinsu.

Ya ƙara da cewa akwai abinda ya shafi haƙƙi na zamantakewa na ɗan’adam da sauran al’amuran ‘yanci akwai guda 32 daga cikin adadin kusan guda 12 ya shafi kamawa da tsare mutum ba bisa ƙa’ida ba. Sannan akwai 15 da yake magana akan rashin adalci wajen gudanar da shari’a.

Alhaji Shehu Abullahi ya ce akwai kuma ɓangare da ya shafi tsangwama ko kuma nuna bambamci guda 25 da ɓangare da ya shafi haƙƙi na samun abin kai wato mallakar abubuwa da walwala ta ɗan’adam wanda a ciki sun samu ƙorafi kusan 273 daga ciki 160 sun shafi haƙƙi ne na lafiya sai kuma guda 75 waɗanda suka shafi haƙƙi na biyan haƙƙi na sallama daga aiki sai kuma guda 35 da suka shafi filaye da gidaje.